19/04/2026
NELFUND Ta Biya Wa Daliba 6,385 na Jami’ar Lafiya Kudin Makaranta Miliyan 795
Hukumar bayar da lamuni ga dalibai ta kasa (NELFUND), ta fitar da kudi har naira miliyan dari bakwai da casa’in da biyar da dubu dari bakwai da ashirin da tara da dari biyar (₦795,729,500) domin biyan kudin karatun dalibai dubu shida da dari uku da tamanin da biyar (6,385) na Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Lafiya (FULafia), Jihar Nasarawa.
Hakan na ƙunshe cikin wata wasikar godiya da jami’ar ta aika wa hukumar ta NELFUND mai dauke da sa hannun Shugaban Jami’ar (Vice Chancellor), Farfesa Mohammed Isa Kida.
A cikin wasikar, jami’ar ta nuna cewa an turo kudaden ne kashi uku tsakanin watan Fabrairu da Maris na wannan shekara k**ar haka:
A ranar 16 ga Fabrairu, 2026, ta biya wa dalibai 4,563 Naira 565,249,500; sai ranar 24 ga Fabrairu, 2026 da aka biya wa ɗalibai 636 Naira 82,189,000; sai kuma 3 ga Maris, 2026 da aka biyawa ɗalibai 1,186 Naira 148,291,000. Jimillar adadin ɗaliban ya k**a 6,385 wanda aka biya musu Naira 795,729,500.
Farfesa Isa Kida ya bayyana jin dadinsa da kuma yabawa hukumar kan yadda take gudanar da ayyukanta cikin gaskiya da rikon amana. Ya ce wannan tallafi babban abin farin ciki ne ga daliban jami'ar, domin zai share musu hawaye tare da basu damar ci gaba da karatunsu ba tare da fargabar kudin makaranta ba.
"Tasirin da NELFUND ke yi a rayuwar dalibanmu ba abin da za a iya kwatantawa ba ne. Mun gode kwarai da gaske kan sadaukarwarku wajen bunkasa ilimi a Najeriya," in ji shi.
Wannan tallafi na zuwa ne a karkashin shirin "Renewed Hope" na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da nufin tabbatar da cewa babu dalibin da ya rasa damar yin karatu saboda rashin hali.