Saifullahi Sani Kubau

Saifullahi Sani Kubau Saifullahi Muhammad Sani

07/11/2025
07/11/2025

Tabbas ʼyan taadda suna kashe musulmi kuma suna kashe kirista,
Suna ƙona masallatai da masallata ,kuma suna ƙona coci da kiristoci.
Su sunkaiwa Trump ƙara , mu kuma mun kaiwa Allah,
Ya kamata a dakatar da kashe-kashe haka a Najeriya.
Mu ci gaba da karanta
(حسبنا الله ونعم الوكيل )
Allah ya saka mana.

19/08/2025

INA YA KAMATA NA KALLA A JIKIN BUDURWATA ?

Tambaya:
Assalamu alaikum,
Malam ko ya halatta in kalli gashin macen da nike so in aura? Ko kuma don Allah malam ka taimaka kaman bayanin abunda ya halatta in kalla a jikin macen da zan aura kafin muyi aure. Na gode. Allah ya gafarta maka.

Amsa:
Wa alaikum assalam To dan'uwa ya halatta ka kalli macen da kake so ka aura, kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda Annabi s.a.w. yake cewa : "Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami damar kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan" Abu dawud a hadisi mai lamba ta : 2082.

Malamai sun yi sabani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin mace lokacin da ya je neman aure :

*1.* Akwai wadanda s**a ce zai kalli fuska da tafin hannu ne kawai, saboda tafin hannu yana nuna ni'imar jikin mace, kamar yadda fuska take nuna kyau, don haka sai a takaita akan su, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai.

*2.* Zai kalli duk abin yake bayyana a jikin mace, don haka bayan fuska da hannu zai iya kallon duga-dugai da wuya.

*3.* Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta juya baya ya kalleta.

Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka mutum zai san yanayin matar da zai aura, yadda ya kamata.

Saidai ba'a son yawaita kallon saboda duk abin da aka halatta saboda bukata, to ya wajaba a tsaya a gwargwadonta, wannan yasa yawaita zuwa zance da yawaita yin waya, zai iya zama haramun saboda yana iya tayar da sha'awa, sha'awa tana iya kaiwa zuwa barna.

Allah ne mafi sani

Don neman Karin bayani, duba : Al'insaf 8\15 da Muhallah 9\161.

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
12/04/2013

18/08/2025

Saka dutse a kabarin mamaci daidai kansa shine Sunnah, hakan Annabi S.A.W. ya yi a kabarin dan uwansa, Usman Ibn Maz’un (RA). Saka itace kuwa, wasu malamai suna cewa ba kyau, domin Annabi ya saka ne a kabari biyu da yace ana yi musu azaba, kai kuma dan uwanka baka da tabbas ana masa azaba. Kuma Annabi S.A.W. yace, za’a sassauta musu azabar kafin itacen ya bushe, mafi yawa kuma a yau, busashshi ake sakawa, don haka ba ma’ana kenan. Wallahu A’alam

NB
Ina nufin itacen da ake sakawa bayan an binne mamaci kamar yadda ake saka dutse, ba wanda ake sakawa kafin a saka kasa ba.

Dr Jabir Sani Maihula

18/08/2025

"Kada ki raina irin baiwar da Allah Ya yiwa mijinki; ko anfi shi kyau ko kudi ko ilimi ko matsayi. Da zarar kina hango baiwar da Allah Ya yiwa wasu mazaje kina raina ta mijinki, ba zakiji dadin zaman aure ba. Kuma ta yiyu mijinki ya fi wadancen dadin zama da iya mu’amala".
✍🏽
Dr. Jabir Sani Maihula

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Saifullahi Sani Kubau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share