28/06/2026
Akwai darasi a wannan hoton kabarin na wani mutum mai suna Mai Ali Dogo.
An haife shi: 1908
Ya rasu: 1935
Ya rayu a duniya na tsawon shekara 27 kacal, yana matashi ya rasu.
Yau muna shekarar 2026.
Idan muka lissafa: Daga 1908 zuwa 2026 = shekara 118 kenan da haihuwarsa.
Daga 1935 zuwa 2026 = shekara 91 kenan yana cikin kabari. InnalilLahi Wa Inna Ilaihirrajuun.
Rayuwarsa a duniya shekara 27 ne kawai, rayuwar kabari kuma shekara 91
Dan'uwa Ka yi tunani...
Mutumin da wata rana yake tafiya, yana magana, yana dariya, yana cin abinci, yana da buri da mafarkai... yau shekaru 91 kenan yana kwance cikin kabari.
Ina gidansa? Ina motarsa? Ina dukiyarsa? Duka babu, abinda ya rage masa shine ayyukansa.
Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa:
"Ko wane rai zai ɗanɗana mutuwa." (Suratul Ali 'Imran: 185)
Ba wanda yasan ranar da zai mutu.
Wata rana kai ma za'a ɗauke ka daga gidanka, a yi maka wanka, a yi maka jana'iza, a kai ka kabari, sannan mutane su koma gidajensu, kai kuma a barka kai kaɗai a kabarinka tare da ayyukanka.
Ko da mutum bai mutu ba a yanzu har sai da yakai ranar tashin alƙiyama, to zai kasance a kabari har zuwa ranar da Allah Ya ƙaddara a busa ƙaho.
Ka tambayi kanka, me ka tanadar domin zaman kabarinka?
Allah Ka kyautata ƙarshenmu, Ka yalwata kaburburanmu da haske, Ka gafarta mana zunubanmu, Ka sa mu kasance cikin bayinka na ƙwarai.
Amin Ya Rabbal 'Alamin.