31/05/2025
RASUWAR MATASA 21 DA S**A WAKILCI KANO A GASAR WASANNI TA KASA SAKAMAKON HATSARIN MOTA WANI BABBAN GIBI NE MAI WUYAR CIKEWA - Sarkin Kano Alhaji Aminu Bayero
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana alhininsa da samun labarin rasuwar Yan wasan da s**a wakici jihar Kano a Gasar wasanni ta kasa da aka gudanar a garin Abekuota dake jihar Ogun.
A safiyar yau ne dai Asabar aka tashi da hatsarin motor data dakko Yan wasan inda sakamakon fadawar motar cikin wani rami, Yan wasan su 21 s**a rasu wasu Kuma s**a jikkata.
Hatsarin dai ya faru ne a garin Dakatsalle dake yankin karamar Hukumar Garun Malam anan jihar Kano gab da karasowarsu cikin birnin Kano.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana rasuwar matasan da cewa wani babban rashi ne bawai ga iyalansu ba harma da al'umar jihar Kano baki daya.
Yayi addu'ar Allah ya jikansu ya gafarta musu ya Kuma baiwa iyalansu hakurin jure wannan babban rashi yasa aljanna makoma a garesu.
Haka kuma mai martaba sarki yayi addu'ar wadanda s**a samu raunuka.Allah ya tashi kafadunsu.
Sa hannu
Abubakar Balarabe Kofar Naisa.