15/07/2026
SHUGABAN ƊARIƘAR ƘADIRIYYA NA AFIRKA YA ZIYARCI GWAMNAN JIHAR KANO: SHEKARU DA DAMA ALAƘAR GIDAN ƘADIRIYYA DA GWAMNATI NA CI GABA DA ƘARA ƘARFI:
Daga Ali Rabiu Sufi
A Daren Jiya, Talata 14 Ga Watan Yuli, 2026, Shugaban Ɗariƙar Ƙadiriyya Na Afirka, Khalifah Sheikh Dr. Ƙaribullah Sheikh Nasiru Kabara, Ya Kai Ziyarar Girmamawa Da Ƙarfafa Zumunci Ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, A Birnin Abuja.
Wannan Muhimmiyar Ziyara Ita Ce Ta Farko Tsakanin Shugabannin Biyu A Hukumance Tun Bayan Zaɓar Eng Abba Kabir Yusuf A Matsayin Gwamnan Jihar Kano, Kuma Ziyarar Ta Zo Ne A Loƙacin Da Gwamnatin Jihar Kano Ke Cigaba Da Gudanar Da Ayyukan Raya Ƙasa Da Kyautata Rayuwar Al'umma.
A Yayin Ganawar Sheikh Dr. Ƙaribullah Ya Taya Mai Girma Gwamna Murnar Nassarorin Da Gwamnatinsa Ta Samu, Tare Da Yi Masa Addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya Ƙara Masa Hikima, Basira, Lafiya Da Dacewa Wajen Jagorantar Al'ummar Jihar Kano.
Kamar Yadda Kowa Ya Sani Gidan Ƙadiriyya Yana Cigaba Da Riƙe Matsayinsa Na Cibiyar Ilimi, Tarbiyya Da Wayar Da Kan Al'umma. Saboda Haka, Sheikh Dr. Ƙaribullah Ya Jinjina Wa Gwamnatin Jihar Kano Bisa Ayyukan Da Take Gudanarwa A Fannonin Ilimi, Lafiya, Gina Ababen More Rayuwa Da Sauran Muhimman Sassa, Inda Ya Ƙarfafa Gwamnatin Da Ta Cigaba Da Wannan Kyakkyawan Tsari.
Haka Kuma Ya Tabbatar Da Cewa Gidan Ƙadiriyya Da Miliyoyin Mabiya Ɗariƙar Ƙadiriyya Za Su Cigaba Da Tsayawa Cikin Addu'a Domin Samun Zaman Lafiya, Haɗin Kai Da Cigaban Jihar Kano Da Ƙasa Baki Ɗaya.
A Nasa Jawabin, Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Nuna Jin Daɗinsa Bisa Wannan Ziyara, Inda Ya Bayyana Cewa Alaƙar Da Ke Tsakanin Gwamnati Da Malamai Babban Ginshiƙi Ce Na Samun Nassarar Duk Wata Gwamnati. Ya Kuma Yi Kira Ga Mabiya Ɗariƙar Ƙadiriyya Da Sauran Al'ummar Musulmi Da Su Cigaba Da Yi Wa Shugabanni Addu'a Domin Samun Zaman Lafiya, Haɗin Kai Da Cigaban Najeriya.
Ƙarin Bayani:
Babu Shakka, Wannan Ziyara Ta Sake Nuna Wani Babban Tarihi Da Ya Daɗe Yana Wanzuwa Tsakanin Gidan Ƙadiriyya Da Masu Mulki. Tun Daga Zamanin Sheikh Umar Kabara, Zuwa Sheikh Ibrahim Na Tsugune, Sheikh Dr. Nasiru Kabara, Har Zuwa Wannan Zamani Na Khalifancin Sheikh Dr. Ƙaribullah Sheikh Nasiru Kabara, Wannan Alaƙa Tana Cigaba Da Tafiya Da Wanzuwa Cikin Mutunta Juna, Bayar Da Shawara, Addu'a Da Kuma Taimakawa Wajen Gina Al'umma Da Cigaban Ƙasa.
Abin Da Ya Kamata A Fahimta Shi Ne, Gidan Ƙadiriyya A Kowane Loƙaci Yana Cigaba Da Riƙe Matsayinsa Na Jagoranci A Fannin Addini, Tarbiyya, Ilimi Da Kuma Bayar Da Shawara Wajen Gina Ƙasa Da Kuma Al'ummar Ƙasar, Domin Samun Zaman Lafiya Da Cigaban Al'umma.
Muna Roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya Ƙara Tsare Mana Shugabannin Ya Haɗa Zukatansu, Ya Basu Ikon Sauke Amanar Da Aka Ɗora Musu, Ya Kuma Cigaba Da Wanzar Da Zaman Lafiya, Haɗin Kai Da Cigaban Jihar Kano Da Najeriya Baki Ɗaya Saboda Girman Shugaba Sallallahu Alaihi Wasallama.
Qadiriyya Media Team
Laraba 15/07/2026.