22/09/2025
Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Dr. Muhammadu Sanusi II, CON, ya halarci taron Unstoppable Africa Conference a gefen babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80. Taron ya mayar da hankali kan damar Afirka wajen bunƙasa mai ɗorewa da kuma haɗin gwiwar ɓangaren masu zaman kansu don cimma manufofin cigaban duniya (SDGs).
A gefen taron, Mai Martaba ya gana da Sarauniyar Netherlands, Máxima, Jakadiyar Musamman ta Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya kan Hada-hadar Kuɗi Mai Ƙunshe da Jama’a, inda s**a tattauna batutuwan shigar da jama’a cikin harkokin kuɗi, ilimi da ƙarfafa mata.
Haka kuma, tare da rakiyar Sarkin Ban Kano, Dr. Mansur Muhtar Adnan, da Sarkin Fulanin Gombe, Alhaji Umaru Kwairanga, Mai Martaba ya ziyarci Hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya domin muhimman tattaunawa kafin babban zaman majalisar.
Sunday, 21st September 2025.