07/07/2025
_*ALBISHIRIN KU MARUBUTA DA MASU SAURARON TASHAR LIMAMIN TSAKAR GIDA?*_
_*SHIN KO KUNSAN TASHAR TA SHIRYA MUKU WANI KYAKKYAWAN TSARI DAN JIN DAƊIN KU?*_
_*KU MARMATSO KUJI*_
Fitattun karshen shekara, wani shiri ne da Tsakar Gida media ta shirya, wanda zata fara gabatarwa a ɗaya daga cikin tashoshin ta dake kan YOUTUBE wato Limamin Tsaka Gida.
Wannan shiri zai tantance daɗaɗan labaran novel guda goma da zamu fara karantawa daga farkon watan August zuwa karshen shekara, wanda a cikin goman za'a fidda uku da s**a fi samun LIKES a kashi goman farko na kowanne labari. Ma'ana shafuka goma da s**a fara sauka.
Abin nufi, koda labari ya bada har zuwa kashi 30 ko 40 to kashi goma na farko kawai za'a lissafa likes din da aka samu, duk abin da ya biyo baya kuma baya cikin lissafi.
Ga mai buƙatar aiko da novel ɗinsa ko novel ɗinta zai iya aikowa ta wa'annan numbobin 07065283730 ko 07049873899 idan ya cika wayannan ka'idoji
KA'IDOJI:
-Dole ne novel ya kasance babu batsa a ciki.
-Novel ya kasance wata tashar bata ɗora shi a YouTube ba.
-Novel ya kasance ya samu kyakykyawan rubutu da aka yi da ka'idojin rubutu.
-Novel ɗin ya kasance document ne ba shafukan WhatsApp ko link ɗin wattpad ba
Sai a turo da takaitaccen bayanin abinda labarin ya kunsa da bai gaza sakin layi uku ba.
Bayan gama tantance labarai goma da zamu karanta, zakuma muyi tsari da marubutan yadda zamu tsara labaran da zamu fara karantawa a farko, idan kuma an kammala gasar za'a bada wata ɗaya domin irga sak**ako.
Ga masu sauraro suma ba'a barsu a baya ba, domin kuwa duk wanda ya riga yin comment za’a dinga pinning na comment ɗin a farko, a karshen gasar wanda comment ɗinsa ya fi zuwa a farko zai samu kyauta.
Haka zalika wanda yayi comment mai ma'ana da ya samu likes mafi yawa shima zai samu kyauta.
Labari zai dinga zuwa ne kowacce rana da misalin karfe 8:00 pm banda ranar juma’a, a tashar YouTube ta Limamin Tsakar Gida.
Allah ya bawa mai rabon sa’a
Ga Mai neman Karin bayanin zai iya tuntubar
Umar Mai Sanyi ko
Khadija Abdullahi Hajjace.
Ko ta dm ga tashoshin Tsakar Gida na Facebook Instagram da tiktok