Aminu Nuruddeen Amin

Aminu Nuruddeen Amin Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Aminu Nuruddeen Amin, TV Channel, Kano.

26/10/2018

The arrival of Jafar Jafar at kano.

Sarkin Kano Ado: Adalin Sarki Allah Ya jaddada Rahama.Ance wata rana sarkin Kano Ado ya dawo daga tafiya, ya biyo ta Kat...
02/10/2018

Sarkin Kano Ado: Adalin Sarki Allah Ya jaddada Rahama.

Ance wata rana sarkin Kano Ado ya dawo daga tafiya, ya biyo ta Katsina Road, sai yake cewa Sarki Waziri (Danrimi), akwai wani gida na anan, da na mallaka tun kafin in zama sarki, amma ban kara waiwayarsa ba, ban sani ba ko zan gane shi?! Sarki Waziri yace " Allah ya taimaki sarki, sai sai inzo in duba" sarki yace "gidan kane? Gida nane, zan zo in duba kayana da kai na.

Bayan yan kwanaki, rannan da dare sai sarki ya sa aka kira masa Danrimi, yace masa yazo ya raka shi unguwa. S**a tafi, Danrimi na jan mota, sai Katsina Rd, su shiga nan, su shiga nan, har s**a zo daidai wani gida. Sarkin Kano ya umarci Danrimi ya tsaya, yace masa "ai kuwa wannan ne gidan, tabbas"

S**a fito, s**a saka akayi musu sallama da maigidan cikin dare. Maigidan ya fito, s**a gaisa. Sarkin Kano ya kalle shi yace " wannan gidan ka ne?" Yace "eh" yace masa saya kayi ko kuma baka akayi? Yace gaskiya asali gidan mahaifinmu ne muka gada. Sarki yace masa " kai dan wane ne( ya fadi sunan maigidan), yace eh. Kafin ya mutu bai bar muku wasiyya ba? Sarki ya tambayi maigidan. Yace "eh ya bar mana wasiyya, yace gidan nan na wani mutum ne Malam Ado".

Sarki yace masa " to nine malam Ado, kuma ba zuwa nayi don in tashe ku ba, na sayi wannan gida sama da shekara 40 da s**a wuce, kuma ni na saka mahaifinku a ciki, Amma abinda nake so da kai, gobe kazo fada, muje gaban sarki da kai, saboda a tabbatar da wannan magana, komai ayi shi da hukuma yafi amfani. Amma kar ka ji komai, ba tashinku zanyi ba". Maigidan ya amsa yace "to Allah ya kaimu". Sarki yace masa, In kazo ka nemi Sarki Waziri, zai kaimu gaban sarki da kai, sai a tabbatar da maganar.

Da safe maigida ya tafi fada, yaje ya nemi Sarki Waziri, aka kai shi office din sarki waziri. Ya gabatar da kansa, sarki Waziri yace " kaine?" Yace "eh nine" yace "to jira"

Da sarki ya zauna a fada aka kira bawan allahnan, shi dai yana ta zura ido baiga malam Ado ba. Har aka kai shi gaban sarki.

Sarki yace masa " kaine muka je gidan ka jiya?" Mutum ya gyara zama, ya kasa magana, saboda bai taba zaton Malam Ado sarkin Kano bane. Sarki yace masa " to nine malam Ado. Gida nane. Ni na saka mahaifinku a ciki. Kuma mun ji dadi da ka rike wasiyyar mahaifinka. (Shi dai mutum yayi kasake, ya kasa cewa komai). Sarki yace " Allah ya shi ma albarka". Nan da nan fada ta dauka " Allah ya shima albarka inji sarki"!!!!

Sarki yace ku nawa ne mahaifinku ya bari, yace " mu bakwai ne: uku maza hudu mata" sarki yace "to yanzu in aka bar maka wannan gida an hada ka rigima da yanuwanka, saboda haka; kaje ka nemo gida a saya maka, su kuma kannenka maza a bar musu wannan gidan su raba. Yanuwanka mata kuma , ku kula dasu, kar ku bar su; su shiga wani hali.

Ance mutumin nan, saboda murna a kasa ya koma gida.

Allah ya jikan sarkin Kano Ado, Allah ya karfafi bayansa. Shi ko na yanzu , Allah yayi mai rabo mai yawa.

A wani Bincike da masana sirrin zaman aure s**ayi, Sungano cewar Budurwar da tadade batayi  auruba da bazawar da ta Dade...
01/10/2018

A wani Bincike da masana sirrin zaman aure s**ayi, Sungano cewar Budurwar da tadade batayi auruba da bazawar da ta Dade tana zawarci sunfi, yanmata sanin darajar miji idan akayi aure. Menene Raayinku. ?

Wanna shi ake kira ayu.
21/09/2018

Wanna shi ake kira ayu.

Remember i posted pictures some months ago of this the Kenyan lady  who found her childhood friend on the streets suffer...
21/09/2018

Remember i posted pictures some months ago of this the Kenyan lady who found her childhood friend on the streets suffering from drug addiction and took him to rehabilitation.??
Take a look to his journey to rehabilitation and the awesome results on how he looks now.Which other way can we define true love??

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Aminu Nuruddeen Amin posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category