24/10/2025
Yakamata ’Yan Najeriya su Jinjina wa Janar Christopher Musa Bisa Sadaukarwarsa ga Tsaron Ƙasa
A lokacin da ƙasarmu ke fuskantar ƙalubale daban-daban na tsaro, ba za a manta da rawar da tsohon Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa (rtd), ya taka ba. Mutum ne da ya sadaukar da lokacinsa, ƙwarewarsa, da rayuwarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasa — a lokacin da ake bukatar irin wannan jarumtaka fiye da kowane lokaci.
Janar Musa, wanda ya shahara wajen gaskiya, ladabi, da kishin ƙasa, ya yi fice a matsayin jagora mai hangen nesa. A matsayinsa na Hafsan Hafsoshin Tsaro, ya nuna ƙwazon haɗa kai tsakanin rundunonin tsaro domin samar da aiki ɗaya na bai daya. A karkashinsa, an samu ƙarin daidaito tsakanin sojoji, ’yan sanda, da sauran jami’an tsaro wajen yaki da ta’addanci da rashin tsaro a yankuna daban-daban na ƙasar nan.
Ba kowane shugaba ke iya ɗaukar nauyin da irin nasa ba. Sadaukarwarsa ta fita fili — daga tunkarar matsalolin Arewa maso Gabas, zuwa ƙoƙarin farfaɗo da tsaro a Arewa maso Yamma da sauran sassan ƙasa. Ya jagoranci aikin tsaro da natsuwa, ba tare da neman yabo ko nuna girman kai ba. Wannan hali ne da ya sa ake ganin ya bar tarihi mai kyau a rundunar sojojin Najeriya.
Yanzu da ya kammala aikinsa, lokaci ne da ’yan Najeriya su nuna godiyarsu da jinjina ga irin gudunmawar da ya bayar. Irin mutanen da s**a sadaukar da kansu don kare ƙasa su ne ginshiƙan da ƙasa ke dogaro da su wajen dorewar zaman lafiya da ci gaba.
A ƙarshe, wannan bai kamata ya kasance ƙarshen hulɗar al’umma da irin waɗannan jarumai ba. A’a, ya kamata gwamnati da ’yan ƙasa gaba ɗaya su ci gaba da amfani da ƙwarewarsu da shawarwarinsu don gina ƙasar da kowa zai yi alfahari da ita. Janar Christopher Musa ya riga ya ba mu misali — misalin kishin ƙasa, aiki da gaskiya, da jagoranci mai hangen nesa.
Arewa post 24