24/12/2025
Ana fargabar mutane da dama sun rasu yayin da dan kunar bakin wake ya tada bom a Masallaci a Maiduguri
An rawaito cewa daruruwan masu ibada sun rasa rayukansu bayan wani ɗan kunar bakin wake ya tayar da bam a masallacin Juma’a na Gambarou da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa wasu daga cikin masu ibadar da s**a tsira daga harin sun ce maharan sun shiga masallacin a ɓoye, sannan s**a tayar da bam ɗin ne a lokacin sallar Magariba tare da jama’a.
“Ɗan kunar bakin waken ya tayar da bam ɗin ne a raka’a ta farko ta sallar Magariba. Mutane da dama sun mutu, wasu kuma sun jikkata da raunuka iri-iri,” in ji wani da ya tsira.
Sai dai ba a samu wanda ya ɗauki alhakin harin nan take ba, amma ana zargin ƙungiyar Boko Haram da aikatawa, kasancewar ta ƙaddamar da hare-haren kunar bakin wake da dama a yankin cikin ‘yan watannin da s**a gabata.