17/10/2021
KANO UPDATE: Jamiyyar APC ta kasa ta goyi bayan Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam'iyyar na jihar Kano.
Daraktan yada labaran jam'iyyar APC na kasa, Alhaji Salisu Na'inna Danbatta ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio Kano.
Danbatta ya ce, tsarin jamiyyar shi ne duk inda ta ke da Gwamna to shi ne jagoran jam'iyya.
Saboda haka duk inda aka yi zabe sabanin wannan to ba halastacce bane, kuma ya saba da tsarin jam'iyyar APC.
Ya kara da cewa "Gwamna ko mai babban mukami idan bamu da Gwamna a jiha shi ne gaba a jam'iyya, a duba a gani wane zabe ne aka yi shi a inda hukumar zabe ta turo wakilai?".
"Wane zabe ne jami'an tsaro s**a je s**a tabbatar da tsaro a wajen? Wannan shi ne sahihin zaben da muka sani a jihar Kano."
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan zaben shugabannin jam'iyyar APC na jihohi wanda ya bar baya da kura a wasu jihohin Najeriya.
An samu rabuwar kai a jihohin Neja, Kwara, Legas da kuma jihar Ogun da sauran su.
A nan Kano ma tsagin Gwamna Ganduje ya gudanar da zabensa tare da ayyana Alhaji Abdullahi Abbas a matsayin wanda ya yi nasarar zama shugaban jam'iyyar ta APC.
A daya bangaren shi ma tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya jagoranci nasa wanda ya ayyana Alhaji Ahmadu Haruna Danzago a matsayin sabon shugaban jamiyyar.