26/07/2025
Ministan Ayyuka na Tarayya, Sanata Dave Umahi, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu Yana da cikakken kuduri na ci gaba da gina dukkan sassan Najeriya ba tare da nuna bambanci ba, Yana mai jaddada cewa an kuduri aniyar tafiya da gaskiya da adalci wajen rabon ayyukan cigaba a fadin ƙasa.
Sanata Umahi ya bayyana hakan ne a martani ga kalaman tsohon Gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya zargi gwamnatin Tinubu da fifita yankin Kudu fiye da Arewacin ƙasar.
“Shugaba Tinubu ya jajirce wajen ganin kowanne yanki ya ci gajiyar dimokuradiyya. Gwamnatinsa na aiki da kowane yanki bisa gaskiya da daidaito, ba tare da nuna bambancin siyasa, yare ko addini ba,” in ji Minista Umahi.
Ya ce ma’aikatarsa tana aiwatar da manyan ayyuka na tituna a sassa daban-daban na Arewa da Kudu, ciki har da sabunta manyan hanyoyi da ke haɗa jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da sauran sassan ƙasar.
Ministan ya kara da cewa zargin nuna wariya a rabon ayyuka na iya haifar da rashin fahimta da rashin hadin kai, yana mai kira ga shugabannin siyasa da su rika duba abubuwa ta fuskar ƙasa baki ɗaya, ba yankin kansu kadai ba.