17/06/2024
MAI LAFIYA ƊAN GATA: KULAWAR DA MAI JUNA BIYU KE BUƘATA
Jama'a barkan mu da warhaka, sannunmu da sake saduwa acikin shirin "Mai Lafiya Ɗan Gata". A cikin shirin mu da ya gabata munji irin sauye-sauyen da jiki ke samu bayan shigar juna, a shirin mu na yau zamuyi duba ga irin kulawar da ya k**ata a baiwa mace juna.
Kamar dai yadda mafiya yawanmu muka sani, mace mai juna biyu tana buƙatar kulawa ta musamman daga ita kanta, makusantanta da jami'an kiwon lafiya. A saboda haka ne ma zamu karkasa yanayin kulawar zuwa gida uku, k**ar haka:
KULAWAR DA MACE MAI JUNA TAKE BUƘATA DAGA JAMI'AN KIWON LAFIYA
Kamar yadda muka faɗa a shirin da ya gabata, mai juna zata fara ziyartar likita tunda daga lokacin ta farga cewa ta samu juna har zuwa haihuwa. Amma kuma ana buƙatar tayi wasu gwaje-gwaje domin sanin lafiyar ta kuma domin kare juna biyun. Waɗannan gwaje-gwaje sun haɗa da:
1. Dunƙulallen Gwajin fitsari: Ana yin dunƙulallen gwajin fitsari domin sanin ko mai juna tana ɗauke da wasu cututtuka masu illa, k**ar 'preeclampsia' (samun sinadarin protein ne yake alamta cewa za'a iya samun wannan larura). Da sauransu.
2. Gwajin 'genotype' idan da ba'a yi ba.
3. Gwajin jini domin sanin rukunin jini da 'Rhesus factor' domin
maganin kota-kwana.
4. Gwajin jini na cututtuka k**ar su hepatitis, ƙanjamau (HIV), ciwon daji, ciwon siga da sauransu.
5. Gwajin tsanaki domin sanin ko akwai ciwon sanyi na 'pelvic inflammatory diseases'. Wannan ciwo kan lalata cikin, ya zube.
6. Gwajin hoto domin sanin matsayin jiki da lafiyar yaron. Da sauransu.
Sannan kuma a ganawarta da likitan ne mace mai juna zata samu shawarwari akan tsarin rayuwarta k**ar:
-Ragewa ko daina shan barasa.
-Barin shan taba sigari da kuma gujewa zama kusa da masu shan sigarin.
-Gujewa shan magunguna barkatai, ba tare da shawarar ƙwararru ba.
-Da sauransu.
KULAWAR DA MACE MAI JUNA TAKE BUƘATA A KARAN KANTA
Akwai abubuwa da yawa da mace mai juna zata yi domin kula da lafiyarta dama ta ɗan cikin nata. Kamar kula da abincinta, shan magungunan ƙarin kuzari k**ar su 'folic acid' da 'ferrous sulphate' waɗanda suke taimakawa wajen samar da jini a jiki.
Abincin da mai juna ya k**ata ta lura da ci sun haɗa da:
-Ganyayyaki, ƴaƴan itatuwa da kuma kayan marmari.
-Abinci mai gina jiki k**ar ƙwai, kifi, nama da sauransu. Waɗannan abinciccika na ɗauke da sinadaran da ake buƙata domin girma da samuwar gaɓɓai ga ɗan cikin nata.
-Kula da shan ruwa yadda ya k**ata, koda kuwa ana samun yawan amai saboda laulayi da sauran su.
Yana daga cikin abubuwan da mai juna zata lura da su da zarar ta samu juna biyu, motsa jiki. Samun juna baya hana mace motsa jiki, musamman idan ba mai yawa bane kuma ba mai cutarwa bane k**ar dambe, kokawa da sauransu.
Mutane da dama na tambaya ko mace mai juna zata iya tarayya da mijinta a bayan ta samu juna biyu. A iya binciken masana, ba'a samu wata illa da saduwa ke kawo ba bayan samun juna biyu tun farkon shigar shi har zuwa haihuwa, musamman idan ana lura da girman cikin, motsin shi da sauransu.
Sai dai yana da kyau a ƙara ɗaukan matan kariya daga cututtuka masu yaɗuwa, k**ar ƙanjamau, ciwon sanyi da sauransu. Sannan kuma bai k**ata ayi tarayya ba idan akwai fitar wani abu k**a daga farin ruwa ko jini ko wani abu mak**ancin haka.
Makusanta nada tasu gudunmawar da zasu iya bayarwa, k**ar 'emotional support' da kuma bata dukkan abun da zai taimaka mata wajen samun cikar abubuwan da muka wassafa a sama tun daga farkon shigar juna har zuwa haihuwa.
Toh bari mu ɗan ja burki a nan. Sai Allah Ya kaimu sati na gaba zamuyi duba ga matsalolin da ka iya samun juna.
Fatan mu, Jalla Sarki Allah Ya sauki masu juna a dukkan inda suke lafiya, Ya basu zuriya ɗayyiba. Allahumma Amin.
© Sulaiman Alkanawiy. 13.12.2020.