10/09/2025
DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Tarayya za ta soke dokar haramta yunkurin kashe kai a Najeriya -inji Gwamnantin Tarayya
Daga Ayau News
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta cire dokar da ke ɗaukar yunkurin kashe kai a matsayin laifi a Najeriya nan da Disamba 2025. Ministan Lafiya, Prof. Muhammad Pate, ya bayyana hakan yayin bikin Ranar Hana Kisan Kai ta Duniya, inda ya ce dokar a yanzu tana jawo hana mutane neman taimako.
Ayau News ta ruwaito Gwamnati ta kafa kwamiti don yin gyaran dokar, wanda ya haɗa da sabunta "Mental Health Act 2021". Sabon tsarin zai mai da yunkurin kashe kai a matsayin matsalar lafiya maimakon laifi.