02/10/2025
Zanga-Zangar Lumana: Mazauna Kano Sun Yi Taron Goyon Bayan CP Bakori, Sun Yaba da Kokarinsa a Fannin Tsaro
A yau wasu mazauna Kano sun fito fili a titunan birnin don gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna goyon bayansu ga Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori.
Masu zanga-zangar sun rike kwalaye da sakonni na yabo da jinjina, suna bayyana cewa CP Bakori ya nuna kwarewa da jajircewa wajen tabbatar da tsaro a jihar Kano, duk da kalubalen da ake fuskanta a fannin tsaro a kasar baki ɗaya.
Shugabannin masu zanga-zangar sun bayyana cewa manufarsu ita ce su nuna wa al’umma da gwamnati cewa ba dukkan jama’a ke adawa da Kwamishinan ba, inda s**a ce kokarin da yake yi wajen magance laifuka da tabbatar da zaman lafiya ya cancanci yabo da kuma karin tallafi daga bangarorin gwamnati.
Wani daga cikin mahalarta, Malam Sani Abdullahi, ya ce: “Mun fito domin nuna godiya ga irin namijin kokarin da CP Bakori yake yi. Mun ga yadda ya hada kai da al’umma da hukumomin tsaro wajen kawo karshen matsalolin tsaro a Kano. Wannan ya nuna cewa muna bukatar irin wadannan shugabanni masu kishin aiki.”
Wannan zanga-zangar ta zo ne kwanaki bayan da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci shugaban kasa da Sufetan ‘Yan Sanda da su dauki mataki kan CP Bakori. Sai dai mazauna da s**a fito yau sun ce su na tare da kwamishinan kuma suna ganin kokarinsa ya kamata a ci gaba da marawa baya