Dandalin Masu Sauraron Radio

Dandalin Masu Sauraron Radio Muna kawo labaran da s**a shafi Aikin jarida cikin Harshen Hausa zalla. Muna maraba da shawarwarin ku
(1)

12/09/2026

Ibrahim Hassan Bako Dambatta kenan yayin da yake karanto labaran dare na Premier Radio Kano a yau Asabar 12/9/2026.

Ku bayyana ra'ayoyinku..

📸 Premier Radio 102.7 FM Kano

Fitaccen ĆŠanjarida kuma shugaban Kafar Siyasarmu TV Aliyu Sufyan Alhassan ya yi kira ga Ć´an jarida da su guji É—aukar cin...
12/09/2026

Fitaccen Ɗanjarida kuma shugaban Kafar Siyasarmu TV Aliyu Sufyan Alhassan ya yi kira ga ƴan jarida da su guji ɗaukar cin zarafi, aibatawa ko wulakanta mutane a matsayin wata alama ta ƙwarewa a aikin jarida.

Ya ce aikin jarida sana’a ce da aka gina kan gaskiya, adalci, binciken sahihan bayanai da kuma bai wa dukkan ɓangarorin da abin ya shafa damar bayyana matsayinsu.

Alhassan ya jaddada cewa aikin É—an jarida shi ne bincika da tantance bayanai kafin wallafa su, tare da gabatar da rahoto cikin adalci da kare mutuncin É—an Adam.

Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan bayyanar wani bidiyon wata ’yar jarida a kafafen sada zumunta, inda ake zargin ta da cin mutuncin wani ɗan siyasa, lamarin da ya sake jawo hankali kan buƙatar bin ƙa’idojin aikin jarida.

Me za ku ce?

11/09/2026

Fatima Kabir Labaran Yakasai kenan yayin da take gabatar da shirin takaitattun labaran dare a yau Juma'a 11/9/2026.

Ku bayyana ra'ayoyinku...

📸 Fatima Kabir Labaran Yakasai

Binta Khalid Mohd ke cigaba da kasancewa tare da ku a zango na biyu na yada shirye-shiryen tashar Premier Radio Kano.Ku ...
11/09/2026

Binta Khalid Mohd ke cigaba da kasancewa tare da ku a zango na biyu na yada shirye-shiryen tashar Premier Radio Kano.

Ku bayyana ra'ayoyinku...

Mahukuntan Hamada Radio da JKD Television sun ce jami’an ƴan sanda sun kai sumame ofishinsu da ke Millennium City a Kadu...
11/09/2026

Mahukuntan Hamada Radio da JKD Television sun ce jami’an ƴan sanda sun kai sumame ofishinsu da ke Millennium City a Kaduna, inda s**a k**a babban manajan tashar, Charles Abah.

A cikin wata sanarwa da s**a fitar ranar Juma’a, mahukuntan tashoshin sun ce jami’an sun shiga ɗakin labaran tashar ne domin neman wata ma’aikaciyar tashar, Zainab Salihu Yabagi.

Sun ce ana neman Zainab ne dangane da wani bidiyo da ta gabatar wanda ya shafi Ibrahim Kabir Masari, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa.

A cewar mahukuntan tashoshin, jami’an ba su samu Zainab ba, amma daga bisani sun k**a babban manajan tashar, Charles Abah, tare da tafiya da shi shalkwatar ƴan sanda da ke Kaduna.

Mahukuntan tagwayen tashoshin sun nuna damuwa kan yadda s**a ce jami’an sun gudanar da samamen, tare da yin kira ga hukumomin da abin ya shafa da su binciki lamarin.

Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Matashin É—anjarida Abdulrahman Salihu, wanda aka fi sani da Abu Talatu, ya samu aiki a sashen Hausa na BBC.Abdulrahman, ...
10/09/2026

Matashin É—anjarida Abdulrahman Salihu, wanda aka fi sani da Abu Talatu, ya samu aiki a sashen Hausa na BBC.

Abdulrahman, ɗan asalin jihar Bauchi, na daga cikin matasan ’yanjarida masu ƙwazo, kuma kafin samun wannan sabon aikin yana aiki da tashar Now FM da ke Legas.

Abu Talatu Ya tabbatar da samun aikin ne ta wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Bayan sanarwar, ’yan uwa da abokan aikinsa sun ci gaba da taya shi murna tare da yi masa fatan alheri a sabon matakin da ya taka a aikin jarida.

Me za ku ce?

Hukumar gudanarwar Premier Radio 102.7 FM Kano ta karrama Kamal Umar Kurna, a matsayin Gwarzon Ma’aikacin Tashar na wata...
10/09/2026

Hukumar gudanarwar Premier Radio 102.7 FM Kano ta karrama Kamal Umar Kurna, a matsayin Gwarzon Ma’aikacin Tashar na watan Satumba 2026.

Kamal na daga cikin ma’aikatan tashar da ke gudanar da ayyuka a sassa daban-daban, ciki har da shirya rahotanni, tace labarai, shirye-shiryen siyasa da gabatar da shirye-shirye.

Bayan karramawar, Kamal ya gode wa Allah, tare da yabawa shugaban Premier Radio, Malam Abba Dabo, bisa amincewa da gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban tashar.

Ya kuma gode wa abokan aikinsa da masu goyon bayansa bisa haɗin kai da ƙarfafawar da suke ba shi, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen wannan nasara.

Me za ku ce?

09/09/2026

Fatima Kabir Labaran Yakasai kenan yayin da take karanto takaitattun labaran dare a yau Laraba 9/9/2026.

Ku bayyana ra'ayoyinku...

📸 Fatima Kabir Labaran Yakasai

09/09/2026

Amina Umar Kafinta kenan yayin da take karanto takaitattun labarai na tashar Premier Radio Kano.

Ku bayyana ra'ayoyinku...

📸 Amina Umar Kafinta

Bayan bankwana da Freedom Radio, Samira Sa’ad Zakirai ta wallafa saƙon godiya ga abokan aikinta, shugabannin tashar da k...
08/09/2026

Bayan bankwana da Freedom Radio, Samira Sa’ad Zakirai ta wallafa saƙon godiya ga abokan aikinta, shugabannin tashar da kuma masu sauraro bisa irin goyon baya, ƙauna da fahimtar da s**a nuna mata tsawon shekarun da ta yi tare da su.

Address

Nassarawa G. R. A
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dandalin Masu Sauraron Radio posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category