11/08/2026
SHIN AN MANTA DA MU NE? — SAƘO DAGA ABBA KABIR YUSUF PROJECT PROMOTION ADVOCATES
Akwai lokacin da yin shiru yake zama ladabi, amma idan shiru ya yi tsawo, mutane na iya ɗauka cewa babu abin da ke damunmu. Mu a Abba Kabir Yusuf Project Promotion Advocates – Facebook Media Team, mun daɗe muna yin shiru ne saboda mun fahimci cewa aikinmu shi ne tallata manufofi, ayyuka da nasarorin Gwamnatin Jihar Kano, ba wai yin korafi ko neman alfarma ba. Mun yi aiki cikin haƙuri, juriya da kishin wannan gwamnati, kuma mun ci gaba da aikimmu ko da kuwa a lokuta da dama ba a tuna da mu ba.
Amma a yau tambayar da muke son yi ita ce: shin masu ruwa da tsaki a cikin wannan gwamnati sun manta da wannan ƙungiya ne, ko kuma saboda ba mu cika yin hayaniya da neman rabonmu ba ne ake ganin kamar ba mu wanzu? An raba abubuwa daban-daban ga ƙungiyoyi da masu ruwa da tsaki; an raba tallafi, an raba kayan aiki, an raba babura, an raba filaye da wasu damammaki, amma idan abin ya zo ga Abba Kabir Yusuf Project Promotion Advocates, sai a rasa inda muka shiga.
Ba wai muna cewa dole sai an ba mu wani abu ba ne. Abin da ke ci mana tuwo a ƙwarya shi ne yadda ake iya manta da mu gaba ɗaya duk da irin gudummawar da muke bayarwa. Wannan ƙungiya ba ta bayyana a yau ba. Ayyukanta sun shahara, kuma mutane da dama da suke kusa da gwamnati sun san da ita. Daga Salisu Yahaya Hotoro zuwa Ibrahim Adam, Salisu Kosawa da sauran masu ruwa da tsaki, babu wanda zai ce bai san wannan ƙungiya da irin aikin da take yi ba. Har Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, muna da yakinin cewa yana da masaniya da kasancewar wannan ƙungiya da irin gudummawar da take bayarwa.
Abin da ya fi ba mu mamaki shi ne, kungiyoyi da dama da s**a taso daga baya ko suke aiki a ƙarƙashin wannan tafiya sun samu damar ci gaba da cin moriyar tsarin fiye da mu, alhali mu mun kasance daga cikin waɗanda suke tsaye suna kare manufofi da ayyukan gwamnati a kafafen sada zumunta. Mun tallata ayyuka, mun kare gwamnati a lokutan da ake mata s**a, mun bayyana manufofinta ga jama'a, kuma mun yi hakan ba tare da mun ce sai an ba mu wani abu ba.
Wataƙila laifinmu shi ne ba mu cika yin korafi ba. Wataƙila saboda mun ɗauki aikinmu a matsayin hidima ne, aka ɗauka cewa ba mu buƙatar a tuna da mu. Amma muna son a fahimci abu ɗaya: yin shiru ba yana nufin babu abin da muke ji ba, kuma rashin yin korafi ba yana nufin ba mu cancanci a duba mu ba.
Har yanzu muna tare da Gwamnatin Jihar Kano. Har yanzu muna goyon bayan manufofin Mai Girma Gwamna. Har yanzu muna ganin abin da muke yi a matsayin gudummawa ga wannan tafiya. Amma ya kamata a tambayi kanmu: shin goyon bayanmu ana buƙatarsa ne kawai lokacin da ake son a yaɗa sakon gwamnati, ko kuma mu ma muna da matsayi a cikin tsarin da muke taimakawa wajen tallatawa?
Idan ana ganin wannan ƙungiya ba ta da muhimmanci, ko kuma ba a buƙatar ayyukan da take yi, ba abin kunya ba ne a sanar da mu. Za mu fahimci matsayinmu, mu nemi wata hanyar da za mu ci gaba da bayar da gudummawarmu. Amma abin da bai kamata ba shi ne a bar ƙungiya ta yi aiki tsawon lokaci, ta yi haƙuri, ta yi juriya, ta tsaya tsayin daka wajen kare gwamnati, sannan duk lokacin da wata dama ta taso da ta shafi ƙungiyoyin gwamnati, a manta da ita kamar ba ta cikin tafiyar.
Muna fatan wannan saƙo ba za a ɗauke shi a matsayin tawaye ko adawa ba. Ba adawa muke yi ba; muna neman a duba mu ne. Ba muna neman fifiko a kan wasu ba; muna neman a ba mu gurbin da ya dace da gudummawar da muke bayarwa. Domin idan mutum yana ba da gudummawarsa ga tafiya, yana da kyau aƙalla ya san cewa ana ganin ƙoƙarinsa.
ABBA KABIR YUSUF PROJECT PROMOTION ADVOCATES – FACEBOOK MEDIA TEAM
MUNA TARE DA GWAMNATI, AMMA MUNA SON GWAMNATI TA SAN CEWA MU MA MUNA CIKINTA.