23/07/2025
Rundunar Hisbah ta jihar Kano, reshen ƙaramar hukumar ta sanya Jumaʼa 1 ga watan Ogusta, a matsayin ranar ɗaura auren matasan da s**a taɓa ɗaurawa kansu aure ba tare da sanin iyaye ba, wato Aliyu da Fatima, dukkan su mazauna unguwar Yakasai dake ƙwaryar birnin Kano.
Shugaban hukumar Hisbah a ƙaramar hukumar birnin Kano Hamidan Tanko Alasaka, shi ne ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa da DNN Hausa, yana mai cewa an cimma matsaya tsakanin iyayen yaran da Hisbah, akan cewa za’a ɗaura wannan sabon aure a ofishin Hisbah ta karamar hukumar birni a ranar 1 ga watan Ogusta na wannan shekara.
Akan haka ne hukumar ke neman al’umma su tallafawa masu niyyar yin auren, musamman waɗanda s**a yi alƙawarin bayar da tallafi tun farko. Inda ya ce akwai mutanen da s**a yi alƙawarin bayar da tallafi ga masu shirin zama ango da amaryar amma kawo wannan lokaci tallafin bai zo hannun Hisbah ba.
Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya ne, wasu matasan s**a ɗaurawa kansu aure ba tare da sanin iyayen su ba, saboda tsananin ƙaunar da suke yiwa juna, wanda hakan ne yasa iyayen Fatima garzayawa ofishin Hisbah da manufar a kashe auren, saboda bai cika sharuɗan addinin Islama ba.