19/08/2024
Ana Umartar Duk Wani ko Wata Dan/'Yar Jam'iyyar NNPP Da Ke da Kudurin Yin Takara Ta Shugabancin Karamar Hukuma Ko Kansila da ke Zuwa Nan ba da daɗewa ba a Kowanne Mataki na Ƙasa, Jiha, Ƙaramar Hukuma, Ko a Mazaɓa, Muƙaman Sun haɗa da; Shugabacin Jam'iyya, Commissioner, Special Adviser, M.D, E.S, Shugabancin Riko Na Ƙaramar Hukuma, Kansilan Riko, Coordinators Na CRC, Kwankwasiyya, Lafiya Jari, Kano Proper, P.A, SSA, S.A, SSR, SR, da duka Sauran Mukamai da ba a faɗa ba.
-Duk Wani Ma'aikacin Gwamnati ko a Wata Hukuma Mai Zaman Kanta Kamar Banki Ko Kamfani.
- Da Su Gaggauta ajiye Muƙamin Ko Aikin a Rubuce daga Yau Asabar 17thAugust,2024 Zuwa Karshen Watan da Mu ke Ciki Wato 31stAugust,2024.
-Sannan Ya/Ta Miƙa Kofi Na Takardar Shaidar Barin aikin wato, "Acknowledgement" Ga Jamiyya (Yin Hakan Wajibi ne).
- SAƁA YIN HAKAN BABBAN LAIFI NE GA JAM'IYYAR NNPP.
(2) Abu Na Biyu, An fitar da Manhaja (Guide Lines) Na Shirye-shiryen Zaɓen da zai gabata tun daga farawa har Karewa.
(3) Abu Na uku Shine; An fitar da Sabon Katin Jam'iyyar NNPP Mai Dauke da Sabon Tambarin (Logo) Jamiyyar, wanda Za su taho daga Ƙaramar Hukuma Zuwa Mazaɓu Bisa tsari Mai Kyau, ta Hannun Sakataren Jam'iyya Na Ƙaramar Hukuma.
-Katin Kyauta ne amma da akwai Kudin (Levy) da Bai taka kara ya karya ba daga Kan Naira Dari #100 zuwa abinda ya yi Sama, Musamman ga "Yan Takarkarin Mu, domin Cika Qa'idojin da s**a kamata don Gujewa dukkan wani abinda zai je ya zo a gaba.