Rahoto MEDIA Concept

Rahoto MEDIA Concept News Broadcast Content!

Gwamnan Kano Engr.Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin  Nasiru Salisu Zango a matsayin Mamba a Kwamitin Yaki da Masu Sha ...
22/07/2026

Gwamnan Kano Engr.Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Nasiru Salisu Zango a matsayin Mamba a Kwamitin Yaki da Masu Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi.

Yaune Ranar da tsohon shugaban kasar Najeriya General Muhammadu Buhari ya rasu.
13/07/2026

Yaune Ranar da tsohon shugaban kasar Najeriya General Muhammadu Buhari ya rasu.

El-Rufai ya bukaci ICPC ta janye zargin karya dokar kotu ........... Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ...
08/07/2026

El-Rufai ya bukaci ICPC ta janye zargin karya dokar kotu ...........

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya musanta zargin da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Nasaba da Hakan (ICPC) ta yi masa na cewa ya yi amfani da damar samun kulawar lafiya ta musamman ba bisa ka'ida ba tare da kuma karya dokar kotu.

Cikakken Rahoton Yana:- Daily Nigeria

30/06/2026

A cikin wata tattaunawa ta musamman da wakiliyar mu Asma’u Adam Fulani ta gudanar da ita tare da Mawaki Jadda Garko a shirin ZAUREN MASANA, an tabo muhimman batutuwa da s**a shafi siyasa da tsarin tafiyar da gwamnatin tarayya a Najeriya.

A cikin hirar, Jadda ya yi tsokaci kan wasu al’amura da s**a shafi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman kan batun rabon muk**ai da kuma wasu matakai da ake zargin gwamnatin ta dauka wajen karfafa tsaro da bai wa wasu bangarori kayan aiki a wasu wurare na kasar.

Haka kuma, ya bayyana ra’ayinsa kan yadda yake kallon wadannan matakai da gwamnatin ke dauka, inda ya ce akwai bukatar a ci gaba da nazari da fahimtar yadda ake tafiyar da su domin tabbatar da adalci da daidaito a kasa.

Muna sanar da masu bibiyar mu cewa cikakkiyar hirar tana nan A YouTube din Mu Mai Suna ASMAU FULANI TV, inda za ku ji dukkan bayanin kai tsaye k**ar yadda aka tattauna ba tare da yankewa ba.

Ku biyo mu a:
Facebook: Rahoto Media Concept
YouTube: ASMA’U FULANI TV

Kada ku manta ku danna Follow / Subscribe domin samun sabbin labarai, hirarraki da rahotanni kai tsaye daga tushe.

A cikin wata tattaunawa ta musamman da tashar Rahoto Media Concept, wakiliyarmu Asma’u Adam Fulani ta zanta da wani fita...
30/06/2026

A cikin wata tattaunawa ta musamman da tashar Rahoto Media Concept, wakiliyarmu Asma’u Adam Fulani ta zanta da wani fitaccen mawaki/mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, inda aka tabo batutuwa masu zafi da s**a shafi siyasa, shugabanci da kuma yadda ake tafiyar da mulki a Najeriya a halin yanzu.
A cikin hirar, an yi tsokaci kan batun tallata gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda a hirar ya bayyana ra’ayinsa kan yadda yake kallon wasu abubuwan da ke faruwa a ƙasar, tare da bayar da nasa fahimta kan wasu manyan batutuwa da s**a shafi ci gaban al’umma da kuma tsarin mulki.
Daya daga cikin kalaman da s**a dauki hankali a cikin hirar shi ne inda ya yi magana kan wani tsohon lamari da ya shafi Wutar Sharada, inda ya danganta wasu abubuwa da sunan tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo a matsayin ra’ayi da fahimtarsa kan yadda al’amura s**a kasance a wancan lokaci.

(Wannan dai ra’ayi ne da ya bayyana a cikin hirar, ba hukunci ba ne daga mu a matsayin kafar yada labarai.)

Rahoto Media Concept na jaddada cewa manufarmu ita ce kawo muku sahihan labarai, tattaunawa da ra’ayoyi daga bangarori daban-daban domin bai wa al’umma damar fahimtar abubuwa daga tushe da kuma ra’ayoyi mabambanta.
📌 Muna kira ga dukkan masu bibiyar mu da su kasance tare da mu domin samun cikakkiyar hirar k**ar yadda aka tattauna ba tare da yankewa ba, domin jin cikakken bayanin abin da aka tattauna kai tsaye daga bakin wanda aka yi hira da shi.
🎥 Cikakkiyar hirar za ta fito nan ba da jimawa ba a:
Facebook: Rahoto Media Concept
YouTube: ASMA’U FULANI TV

Ku tabbata kun danna follow / subscribe domin kada ku rasa sabbin abubuwan da muke kawo muku kai-tsaye daga bakin masu ruwa da tsaki.

🌧️ SHIN ANYI RUWA A YANKIN KU?Rahoto Media Concept (RMC) na son jin halin da ake ciki a yankinku bayan ruwan sama da aka...
22/06/2026

🌧️ SHIN ANYI RUWA A YANKIN KU?

Rahoto Media Concept (RMC) na son jin halin da ake ciki a yankinku bayan ruwan sama da aka samu.

Shin an samu ruwa mai yawa kuwa? Ko kuma an samu ambaliya, cunkoson ababen hawa, ko wasu matsaloli da s**a shafi al’umma?

Ku bayyana mana halin da ake ciki a yankinku ta hanyar yin sharhi a ƙasa. Haka kuma idan kuna da hotuna ko bidiyo na yadda ruwan ya kasance, ku aiko mana domin mu wallafa domin sauran al’umma su sani.

Manufarmu ita ce tattara sahihan bayanai daga jama’a domin wayar da kai da kuma sanar da al’umma abubuwan da ke faruwa a sassa daban-daban.

RAHOTO: Ummeetah Yusuf

Fadar Shugaban Nijeriya ta bayyana cewa kiran da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya yi na shugaban ƙasa Bol...
22/06/2026

Fadar Shugaban Nijeriya ta bayyana cewa kiran da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya yi na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauka daga mulki “wasan yara ne” kuma yunƙurin ɗauke hankali ne daga muhimman batutuwan ƙasa.

A cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, gwamnatin ta ce Peter Obi ya yi kuskuren kwatanta tsarin mulkin Nijeriya da na Birtaniya, duk da cewa Nijeriya na amfani da tsarin shugaban ƙasa mai wa’adin shekaru huɗu.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi koyi da Firami...
22/06/2026

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi koyi da Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ta hanyar sauka daga muƙaminsa.

New Media 24 ta rawaito cewa, Obi ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta gaza cika mafi yawan alƙawuran da ta ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe, musamman waɗanda s**a shafi inganta rayuwar 'yan Najeriya.

Ya ce duk da alkawurran da aka yi na kawo sauƙi ga al'umma, har yanzu 'yan ƙasa na ci gaba da fuskantar ƙalubale a fannonin tattalin arziki da rayuwar yau da kullum.

Obi ya jaddada cewa shugabanni ya k**ata su ɗauki alhakin ayyukansu, yana mai cewa duk lokacin da gwamnati ta kasa cimma manufofin da ta ɗauka, ya dace a sake duba matsayinta domin amfanin ƙasa da al'umma.

Jam’iyyar PRP ta musanta rahotannin da ke cewa ta sayar wa Rabiu Musa Kwankwaso, mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na...
22/06/2026

Jam’iyyar PRP ta musanta rahotannin da ke cewa ta sayar wa Rabiu Musa Kwankwaso, mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, fom ɗin tsayawa takara guda 69.

Shugaban masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Arewa maso Yamma, Abdulkadir Musa Guza, ya yi zargin cewa Kwankwaso ya sayi dukkan fom ɗin takarar PRP domin “kwace iko” da jam’iyyar tare da tallafa wa magoya bayansa su yi takara a ƙarƙashin tutar jam’iyyar.

Matar aure ta caka wa mijinta wuka ya mutu a KanoWata matar aure mai suna Fatima, mazauniyar unguwar Rimin Kebe a jihar ...
16/06/2026

Matar aure ta caka wa mijinta wuka ya mutu a Kano

Wata matar aure mai suna Fatima, mazauniyar unguwar Rimin Kebe a jihar Kano, ana zarginta da kashe mijinta Auwalu bayan ta caka masa wuka, ƙasa da watanni biyu da aurensu.

Daily Trust ta rawaito cewa lamarin ya faru ne ranar Lahadi bayan wata takaddama da ta kaure tsakanin ma'auratan.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Daily Trust cewa marigayin ya yi kururuwar neman taimako bayan da matar ta kai masa harin.

Majiyar ta ce Fatima ta yi ikirarin cewa an tilasta mata auren ne, kuma ba ta son mijin nata, inda ake zargin ita ta caka masa wuka a wuya, lamarin da ya janyo masa mummunan rauni har ya kai ga rasuwar sa.

Trust ta rawaito cewa an garzaya da Auwalu zuwa ofishin 'yansanda sannan daga bisani aka kai shi asibiti, amma ya rasu kafin a isa.

Jami'an 'yan sanda na ofishin Zango Police Division da ke Dantamashe sun k**a matar nan take, kuma tana tsare a hannunsu domin ci gaba da bincike.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kakakin rundunar 'yan sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai amsa kira ko sakon tes da aka aika masa ba domin jin ta bakin rundunar kan lamarin.

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Rahoto MEDIA Concept posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share