29/07/2025
Yadda Sauyin Yanayi Ke Jefa Mata Masu Juna Biyu Cikin Hadari"
Daga Safiya Usman
A wani bincike na musamman da aka gudanar, an gano cewa sauyin yanayi, musamman lokacin zafi, na haddasa matsaloli masu tarin yawa ga mata masu juna biyu, inda hakan ke jefa su cikin hadurran lafiya da ke bukatar kulawa ta musamman.
A cikin hirar da muka yi da Hajiya Fatima, wata gogaggiya a fannin kiwon lafiya da wayar da kai kan batutuwan sauyin yanayi, ta bayyana cewa mata da yawa ba su da isasshen ilimi dangane da yadda sauyin yanayi ke shafar lafiyar su, musamman lokacin da suke dauke da ciki.
“Akwai lokacin da mace ke samun canje-canje na jiki saboda juna biyu. Sauyin yanayi, musamman zafi, na kara tsananta lamarin. Mafi yawan matan da ba su da ilimi kan hakan kan fada cikin mawuyacin hali,” in ji Hajiya Fatima.
Zafin Rana Da Hayakin Gawayi Na Kara Dagula Lamura
A cewar Hajiya Fatima, zafi mai tsanani na hana mata masu juna biyu sukuni, kuma hakan na iya janyo hauhawar jini, bugun zuciya da ma faduwar gwiwa. Ta kara da cewa amfani da gawayi wajen dafa abinci, duk da cewa yana saukaka kashe kudi, na iya jefa lafiyar mata cikin hadari.
“Hayakin gawayi yana da illa ga huhu, musamman ga masu ciki. Sannan wahalar hurawa da saurin konewar sa na kara wahalar da mace mai juna biyu,” ta ce.
Ta yi kira ga mazaje da su dinga bai wa matansu kulawa ta musamman, ta hanyar tanadar musu da wuri mai iska, da amfani da hasken rana (solar) domin saukaka zafin daki da kare lafiyar uwargida da jinjirin da ke cikin ta.
Bitar Rayuwar Mata Masu Sana’ar Gurasa a Kwanar Dala
A wani bangare na wannan bincike, Hajiya Fatima ta kai ziyara unguwar Kwanar Dala a Kano, inda ta gana da wasu mata da ke gudanar da sana’ar gurasa. Ta yaba da kokarinsu na jurewa kalubalen sauyin yanayi da hayakin wuta da ke barazana ga lafiyarsu.
“Matan suna yin gurasa ba dare ba rana. Ko da ruwa ya sauka, su kan ci gaba da aiki. Wannan jajircewa ta burge ni matuka,” in ji ta.
Matan sun bayyana cewa suna fuskantar zafin wuta da hayaki, amma babu wata mafita ta zamani da za ta taimaka musu wajen gudanar da sana’ar cikin sauki da kariya ga lafiyarsu.
Shirin Muryarta Raya Muhalli Ya Taimaka
Hajiya Fatima ta bayyana irin rawar da shirin “Muryarta Raya Muhalli” ke takawa wajen wayar da kai kan illolin sauyin yanayi da hanyoyin da za a bi don kare kai. Ta ce ta koyi darussa masu yawa daga shirin, wanda hakan ne ya karfafa mata gwiwar ci gaba da ilimantar da mata a unguwanni daban-daban.
Kira Ga Gwamnati Da Kungiyoyi Masu Zaman Kansu
A karshe, Hajiya Fatima ta bukaci Gwamnatin Jihar Kano da kungiyoyin ci gaban al’umma da su rika kai dauki ga mata masu sana’ar gurasa da sauran al’umma da ke fama da matsin rayuwa sakamakon sauyin yanayi.
"Tallafa wa wadannan mata zai ba su damar amfani da hanyoyin zamani wajen sana’ar su, sannan hakan zai rage hadurran lafiyar da suke fuskanta,” ta jaddada.