11/10/2025
Jerin sunayen Wadanda Gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi wa Afuwa da Sassauci kan hukuncin da aka zartar musu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa manyan fursunoni da tsofaffin fursunoni guda 175 afuwa da sassauci, ciki har da marigayi Major Janar Mamman Jiya Vatsa, marigayi Ken Saro-Wiwa, “Ogoni Nine”, tare da Maryam Sanda da wasu da dama.
Kwamitin bada shawara kan afuwar shugaban ƙasa, ƙarƙashin jagorancin Ministan Shari’a, Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi ne ya bada shawarar yin afuwa ga tsofaffin fursunoni 15 (11 daga cikinsu sun riga sun rasu), da bayar da sassauci ga fursunoni 82, tare da rage wa’adi ga fursunoni 65. Haka kuma, an mayar da hukuncin kisa ga fursunoni bakwai zuwa daurin rai-da-rai.
Prince Fagbemi ya gabatar da wannan rahoto a taron Council of State ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Cikakken Sunayen Waɗanda Suka Amfana da Afuwa da Sassauci
Waɗanda Aka Yi Wa Afuwa
1. Nweke Francis Chibueze (44) – daurin rai-da-rai saboda kwayar Cocaine.
2. Dr Nwogu Peters (67) – hukuncin shekara 17 saboda zamba tun 2013.
3. Mrs Anastasia Daniel Nwaoba (63) – ta rigaya ta kammala zaman gidan yari saboda zamba.
4. Barr. Hussaini Alhaji Umar (58) – an yanke masa tara N150M a shari’ar ICPC a 2023.
5. Ayinla Saadu Alanamu (63) – an yanke masa shekara 7 saboda cin hanci a 2019.
6. Hon. Farouk M. Lawan (62) – an yanke masa shekara 5 saboda rashawa a 2021.
Waɗanda Aka Yi Wa Afuwa Bayan Mutuwarsu
7. Sir Herbert Macaulay – an hana shi mukaman siyasa a 1913 saboda zargin karkatar da kuɗi ta hannun Turawan mulkin mallaka.
8. Major Janar Mamman Jiya Vatsa – an kashe shi a 1986 saboda zargin juyin mulki.
Ogoni Nine
9. Ken Saro-Wiwa
10. Saturday Dobee
11. Nordu Eawa
12. Daniel Gbooko
13. Paul Levera
14. Felix Nuate
15. Baribor Bera
16. Barinem Kiobel
17. John Kpuine
An kuma yi girmamawa ta musamman ga waɗanda aka kashe a wannan rikici:
• Chief Albert Badey
• Chief Edward Kobaru
• Chief Samuel Orage
• Chief Theophilus Orage
Sassauci da Rage Hukunci
Da