Basheer Maradoon

Basheer Maradoon Media plartform for news and podcast The Page is Unofficial for Bello Matawalle, but it was however Approved by Hon. Bello Matawalle

16/01/2026

I got over 1,000 reactions on one of my posts last week! Thanks everyone for your support! 🎉

YANZU YANZU!Babbar Kungiyar kwalon kafa ta Real Madrid ta Kori kocin ta Xabi Alonso.Hakan ya biyo baya ne bayan wata yar...
12/01/2026

YANZU YANZU!

Babbar Kungiyar kwalon kafa ta Real Madrid ta Kori kocin ta Xabi Alonso.

Hakan ya biyo baya ne bayan wata yar yarjejeniya tsakanin bangarora biyun.

Ya kuke gani wannan matakin na Real Madrid?

07/01/2026

I got over 3,000 reactions on my posts last week! Thanks everyone for your support! 🎉

fans

03/01/2026
DONALD TRUMP YA TABBATAR DA K**A SHUGABAN KASAR VENEZUELA BAYAN KAI HARE-HARE A KASAR.Cikin wani gajeren saƙo da ya wall...
03/01/2026

DONALD TRUMP YA TABBATAR DA K**A SHUGABAN KASAR VENEZUELA BAYAN KAI HARE-HARE A KASAR.

Cikin wani gajeren saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, shugaban na Amurka Donald Trump ya ce a lokacin 'mummunan harin' an k**a Shugaba Nicolas Maduro da matarsa tare da ficewa da su daga ƙasar.

DA DUMI-DUMI:Labarai daga Najeriya suna nuni da cewa Shugaba Bola Tinubu zai canza sunan Najeriya kafin wa’adinsa ya ƙar...
02/01/2026

DA DUMI-DUMI:

Labarai daga Najeriya suna nuni da cewa Shugaba Bola Tinubu zai canza sunan Najeriya kafin wa’adinsa ya ƙare.

Me za ku ce?

CHELSEA TA KORI MAI BAWA YAN KWALLON TA HORO.Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake Ingila ta kore kocin ta Enzo Maresca ...
01/01/2026

CHELSEA TA KORI MAI BAWA YAN KWALLON TA HORO.

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake Ingila ta kore kocin ta Enzo Maresca biyo bayan kasawar sa k**ar yadda kulob din tayi tsammani.

Cikin wasanni bakwai da s**a wuce Chelsea ta samu nasara akan kungiya daya ne kacal.

ABUBUWAN DA KUKE BUQATAR SANI AKAN SABUWAR DOKAR HARAJIN NAJERIYAA yau 1 ga watan Janairun 2026 ne ake sa ran sabuwar do...
01/01/2026

ABUBUWAN DA KUKE BUQATAR SANI AKAN SABUWAR DOKAR HARAJIN NAJERIYA

A yau 1 ga watan Janairun 2026 ne ake sa ran sabuwar dokar haraji ta Najeriya za ta fara aiki wadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saka wa hannu domin amincewa ta zama doka.

An dai ta tunanin cewa za a dakatar da fara aiwatar da harajin kafin sabuwar shekara sak**akon zarge-zargen cushe da aka yi wa dokar ta haraji, wadda aka ce ta bambanta da asalin wadda majalisar dokoki ƙasar ta amince da ita.
A ranar 30 ga watan Disambar 2025 ne shugaba Tinubu ya sanar da cewa babu buƙatar dakatar da fara aiwatar da harajin domin hakan zai katse wa Najeriya burinta na samar da cigaban da ake buƙata.

Sai dai ya ce yana sane da irin zarge-zargen da ake yi dangane da cushe a dokar kuma yana aiki da majalisar dokokin ƙasar wajen samar da mafita.
Yanzu dai abin da al'ummar Najeriyar ke son sani shi ne ta yaya wannan haraji zai shafe su daga ranar 1 ga watan Janirun sabuwar shekarar 2026.

Duk wani É—an Najeriya da ke samun kuÉ—in shiga a Najeriya walau dai ma'aikaci ne ko É—an kasuwa ko masu shirye-shirye a kafafen sada zumunta ko masana'antu ko kamfanoni, za su biya haraji.

Haka kuma dokar ta ce duk wani ɗan Najeriya da ke neman kuɗi a ƙasashen waje amma kuma yana zaune gida Najeriya, to shi ma zai biya wannan haraji.
Sai dai kuma tanade-tanaden dokar harajin sun keɓe duk wanda kuɗin shigarsa bai wuce ₦800,000 a shekara ba daga biyan harajin kuɗin shiga. Wannan yana nufin cewa ma'aikatan da ke karɓar albashi mafi karanci ba za su biya harajin kuɗin shiga ba.

Nawa ne harajin?

Hukumar tattara harajin ta tarayya wato FIRS, wadda yanzu ta koma Nigeria Revenue Service wato NRS, a kundin da ta fitar ta nuna cewa kasancewarku Æ´an Najeriya ba shi ne zai sa ku biya harajin ba illa dai yawan samun da kuke yi, inda ta saka sharaÉ—in da sai mutum ya kai zai fara biyan haraji.

Babu haraji a kan N800,000 ta farko
N2,200,000 za a biya kaso 15 na kuÉ—in
N9,000,000 za a biya kaso 18 na kuÉ—in
N13,000,000 za a biya kaso 21 na kuÉ—in
N25,000,000 za a biya kaso 23 na kuÉ—in
N50,000,000 za a biya kaso 25 da kuÉ—in
Jerin mutane da abubuwan da aka É—auke wa haraji

Bisa kundin hukumar tattara harajin ta Najeriya, an É—auke harajin daga kan wasu kuÉ—ade da mutane k**ar haka:
Mutumin da ke samun kuɗi daidai da albashin ma'aikacin Najeriya mafi ƙanƙanta na N72,000, a wata.
Mutumin da samunsa a shekara bai wuce N1,200,000 ba.
Kyauta (babu haraji a kyauta).
KuÉ—in da mutum ke tarawa na fansho.
KuÉ—in fansho da garatuti.
KuÉ—in insorar lafiya.
Asusun lamunin gidaje.
Riba a kan kuÉ—aÉ—en rance na mutumin da ke cikin gida yake son ya malleke shi.
KuÉ—aÉ—en insora.

KuÉ—in sallamar ma'aikaci daga aiki da ba su wuce N50,000,000 ba.
KuÉ—in da aka sayar da gidan da aka ma'aikaci ya mallaka bayan shekaru yana zaune a ciki.
KuÉ—in da mutum ya sayar da wata kadara da bai wuce N5,000,000 ba.
Sayar da motoci na ƙashin kai da ba su wuce biyu a shekara ba.
Riba a kan hannun jarin da ba ta kai N150,000,000 a shekara ko kuma N10,000,000.

Kuɗaɗen jinƙai da na ƙungiyoyin addini (waɗanda ba don riba aka kafa su ba)
Ƙananan masana'antu da uwar kuɗin jarinsu ba ta wuce N100,000,000 ba ko kuma gabaɗaya jarin bai wuce N250,000,000.
Ƙananan ƴan kasuwa da suke tasawa.

Harajin da aka É—auke kan kayayyaki (VAT) da s**a haÉ—a da:
Kayan abinci.
KuÉ—in haya.
Harkoki da kayan karatu.
Harkar lafiya.
Magunguna.
Ƙananan kamfanoni da ribarsu ba ta wuce N100,000,000 ba.
Fetur, dizel da kayan wuta mai amfani da hasken rana.
Kayan noma - Takin zamani, iri, abincin dabbobi da dabbobi masu rai.

Saye ko lamuni ko hayar kayan aikin gona.
Na'urorin da nakasassu ke amfani da su k**ar abin jin magana da kujerar masu nakasa da abin rubutu makafi.

Sufuri - motar haya wadda ba mutum ne ya É—auke ta shata shi kaÉ—ai ba.
Motoci masu amfani da wutar lantarki da kayansu.
Kayayyakin jinƙai.
Kayan jarirai.
Kayan tsaftar mata . tawul da audugar mata.
Ƙasa da gine-gine.
Harajin da aka É—auke na kuÉ—aÉ—e da bankuna ke cirewa (Stamp duties):
Aikewa da kuÉ—in da bai wuce N10,000 ba.
Albashi.
Aikewa da kuÉ—i tsakanin banki guda.
Aikewa da takardun kuÉ—aden lamuni da hannun jari na gwamnati.
Dukkanin takardun da ke É—auke da hannun jari.
Mutanen da aka yi wa sassauci

Ma'aikacin da albashinsa na shekara bai wuce N20,000,000, zai rinƙa biyan kaso 18 maimakon 25.
Sassaucin kaso 20 a shekara ga (Masu biyan kuÉ—in haya).

Ta yaya za a cire harajin?

Harajin Æ´an kasuwa:
Wannan na ɗaya daga cikin harajin da ake da Harajin Ɗaiɗaiku wato "Personal Income Tax" wanda kuma ƴan kasuwa da masu ƙananan masana'antu ke biya ta hanyar zuwa su zauna da jami'an hukumar tattara haraji domin bayar da bahasi.

Masu biyan wannan haraji kan biya harajin ne a ƙarshen shekara bayan yin la'akari da ribar da uwar jarinsu ta samar musu.
Sai dai kuma bankunan da suke hada-hada a ciki na da damar sanar da hukumar tattara harajin irin hada-hadar da daiÉ—aikuwar ke yi wadda ta kai naira miliyan 25 ko naira miliyan 50 ga kamfanoni.

Harajin ma'aikata - "PAYE"
Shi ma wannan haraji ne da É—aiÉ—aikuwar jama'a da suke biya musamman ma'aikata waÉ—anda suke É—aukar albashi.
A wannan tsarin na biyan haraji da ake kira da biyan haraji daidai samu ko kuma "PAYE", ana cire wa ma'aikata harajin ne a kowane wata kuma daga tushe.
Misali, wasu ma'aikatun da ba na gwamnati ba suna mu'amila da manyan kamfanoni ko kuma ƙwararru kan haraji da kan cire kuɗaden harajin tun daga tushe. Saboda haka shi ma'aikaci ana cire harajin nasa daga tushe k**ar yadda ake yanke kuɗin fansho da na lamunin gida.
Me zai faru da kuÉ—aÉ—en jama'a a asusun banki?

Wannan tambaya ce da ke zuciya da laɓɓan mafi yawan ƴan Najeriya inda ake ta zulumi cewa idan aka fara aiwatar da sabon harajin to bankuna za su rinƙa cire haraji daga asusun mutane.
Wannan ba gaskiya ba ne - babu ruwan banki da kuÉ—aÉ—enku da ke hannunsu walau dai a ajiye a cikin asusu ko kuma masu shige da fice.
Rawar da banki kan taka ita ce kawai su rinƙa sanar da hukumar tattara haraji dangane da shige da ficen kuɗin da s**a kai miliyan 25 ko 50 a duk watanni uku.
Harajin da bankuna za su cire

Bisa wannan sabuwar doka ta haraji, bankuna suna da damar cire haraji na naira 50 a duk hada-hadar da ta kai naira 10,000 zuwa sama, wato kuɗin da aka tura ko kuma a karɓa.
Wannan bayani ma na cikin wasiƙun da bankunan s**a aikewa da abokan hulɗarsu tun kafin ranar 1 ga watan na Janairun 2026.
Wannan tsarin ba zai shafi kuÉ—in albashin mutum da ke shiga asusun bankinsa ba da kuma kuÉ—in da aka tura daga banki iri É—aya.
A baya dai, wanda aka tura wa kudi ne kaÉ—ai ake cirewa wannan harajin, amma yanzu tsarin zai shafi wanda ya tura kuÉ—in ma.
Bankunan sun fayyace cewa wannan haraji ya banbanta da kuɗin da bankuna ke cirewa da aka saba gani ba kuma ake aike wa mutum da saƙo a lokacin da yake tura kuɗi.

An zarge ni da hannu a harkar ta’, duk abunda zasuyi man bazan taba komawa APC ba.Bala Muhammed (Kauran Bauchi)
31/12/2025

An zarge ni da hannu a harkar ta’, duk abunda zasuyi man bazan taba komawa APC ba.

Bala Muhammed (Kauran Bauchi)

KOTU TA TURA MALAMI DA MATAR SA, DA DANDAN SA GIDAN YARIN KUJE.An gurfanar da tsohon ministan Shari’a, Abubakar Malami d...
30/12/2025

KOTU TA TURA MALAMI DA MATAR SA, DA DANDAN SA GIDAN YARIN KUJE.

An gurfanar da tsohon ministan Shari’a, Abubakar Malami da iyalinsa a gaban kotun a ranar Talata, inda s**a bayyana ƙin amincewa da zargin da ya shafi safarar kuɗaɗe da mallakar kadarori ba bisa ƙa’ida ba.

Abubakar Malami ya Hallarci zaman kotu an Abuja yau Talata.Babban Lauyan tarayya kuma tsohon Ministan Shari'a Abubakar M...
30/12/2025

Abubakar Malami ya Hallarci zaman kotu an Abuja yau Talata.

Babban Lauyan tarayya kuma tsohon Ministan Shari'a Abubakar Malami, SAN ya iso kotun koli dake babban birnin tarayya Abuja domin fuskantar tuhuma a gaban Hukumar EFCC.

Malami, dansa da wani mutum, za su fuskanci tuhume-tuhume har goma sha shida da ake zarginsu da hada baki wajen yin zamba da aminci da dukiyar al’umma.

Address

Kano

Telephone

+2348136803030

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Basheer Maradoon posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Basheer Maradoon:

Share