
16/09/2025
Fadar shugaban kasa ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa hauhawar farashin kaya (inflation) a kasar zai ci gaba da sauka, har ya kai zuwa kasa da kaso goma cikin dari wato single digit.
Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin tattalin arziki, Tope Fasua, ne ya bayyana haka a shirin The Morning Brief na Channels TV a ranar Talata.
Fasua ya ce saukar da aka samu a adadin hauhawar farashin kaya ya riga ya fara tasiri a kan farashin kayan abinci, wanda ya fara sauka a kasuwanni.
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar da sabbin alkaluma a ranar Litinin, inda ta nuna cewa hauhawar farashin kaya ya sauka zuwa 20.12% a watan Agusta 2025, idan aka kwatanta da kashi 21.88% a watan Yuli 2025.