Sabuwar muryar Hausa

Sabuwar muryar Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sabuwar muryar Hausa, Digital creator, Kano.

16/08/2026

"Da sana'ar saida tukunya na Ke biyawa yayana makarantar kudi" Matashi ibrahim...

17/07/2026

Yadda ake kaimun Kofi na yan Bori....

16/07/2026

Yadda aka Gudanar da wasan yan Bori a wailari dake jahar kano... ゚

13/07/2026

"YANZU KOWA YA GANE FILM WAIKWAYO NE YUSUF GUGUWA" Acikin Shirin Dawa Muke tare na

08/07/2026

MALAMIN ILMIN TAURARI YA FITAR DA HASASHEN ABUBUWAN DA YA CE ZA SU IYA FARUWA A IRAKI KAFIN ƘARSHEN NUWAMBA 2026

MALAMIN ILMIN TAURARI YA FITAR DA HASASHEN ABUBUWAN DA YA CE ZA SU IYA FARUWA A IRAKI KAFIN ƘARSHEN NUWAMBA 2026Daga Sok...
06/07/2026

MALAMIN ILMIN TAURARI YA FITAR DA HASASHEN ABUBUWAN DA YA CE ZA SU IYA FARUWA A IRAKI KAFIN ƘARSHEN NUWAMBA 2026

Daga Sokoto, Najeriya.
Wani malamin ilmin taurari, Sheikh Abubakar Malam Umar Maisanda, ya fitar da abin da ya bayyana a matsayin hasashen wasu abubuwan da ya ce za su iya faruwa a ƙasar Iraki tsakanin ranar 6 ga Yuli zuwa 30 ga Nuwamba, 2026.

A cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa, Abubakar Maisanda ya ce hasashen nasa ya samo asali ne daga abin da yace Allah Ya bayyana masa, tare da abin da ya danganta da ƙa'idar ilmin taurari.

Ga abubuwan da ya yi hasashen za su iya faruwa:

1. Jam'iyyar da ke mulki za ta iya fuskantar manyan matsaloli da rikice-rikice a cikin harkokinta.

2. Iraki na iya fuskantar ƙalubalen tsaro da fitintinu, ko dai sak**akon rikicin siyasa ko kuma yaƙi. Haka kuma, ya yi kira ga gwamnatin ƙasar da ta ƙara ƙaimi wajen tsaurara matakan tsaro, yana mai cewa za a samu nasarar k**a wasu da ake zargi da aikata ta'addanci.

3. Ya kuma yi hasashen yiwuwar samun hatsurran jiragen sama, ko dai sak**akon hare-haren ta'addanci ko wasu matsalolin da s**a shafi harkokin sufurin jiragen sama.

4. A cewarsa, kafin ranar 30 ga Nuwamba, 2026, ana iya samun sauyin gwamnati ta hanyar juyin mulki ko kuma a k**a shugaban ƙasar. Ya buƙaci hukumomin Iraki su ƙara taka-tsantsan tare da ɗaukar matakan da s**a dace domin tabbatar da zaman lafiya.

5. Haka kuma, ya ce wasu baƙi daga wata ƙasa za su shiga Iraki, lamarin da ya yi iƙirarin cewa na iya haifar da tashin hankali da asarar rayuka. Saboda haka, ya shawarci hukumomi su ƙara sa ido kan masu shiga ƙasar.

6. Maisanda ya kuma yi hasashen cewa wasu 'yan ƙasar za su yi hijira sak**akon matsalolin da ka iya tasowa, yayin da ake iya korar wasu baƙi da ba 'yan ƙasar ba.

7. Ya ƙara da cewa ana iya gudanar da bincike kan wasu manyan mutane a ƙasar, inda za a ƙwace wasu kadarori da kuɗaɗe tare da tsare wasu daga cikinsu.

8. A ƙarshe, ya yi hasashen cewa za a iya samun zanga-zanga a wasu sassan Iraki kafin ƙarshen watan Nuwamba, 2026.

A Lura: Wannan hasashe ra'ayi ne da iƙirarin wanda ya fitar da shi, kuma ba hujja ce da ke tabbatar da cewa abubuwan da aka ambata za su faru ba.

Wane fata kuke yi wa ƙasar Iraki da al'ummarta?

Ana neman mutum biyar masu takardar shaidar karatun Mass Communication (Aikin Jarida), k**ar yadda Usman B. Lawal Rabah ...
06/07/2026

Ana neman mutum biyar masu takardar shaidar karatun Mass Communication (Aikin Jarida), k**ar yadda Usman B. Lawal Rabah ya sanar a shafinsa na Facebook.

Sojojin Nigeria sun k**a wani mutum da ake zargi sojan bogi ne a jahar Katsina.A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar...
06/07/2026

Sojojin Nigeria sun k**a wani mutum da ake zargi sojan bogi ne a jahar Katsina.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce dakarun Brigade ta 17 sun k**a wanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 1:30 na rana a ranar 4 ga Yuli, 2026, bayan sun gan shi sanye da gajeren wando irin na kayan sojoji, lamarin da ya sa s**a tsayar da shi domin bincike.

Wanda ake zargin da aikata sojan bogi ank**ashi ne a ƙaramar hukumar Malumfashi da ke jihar Katsina, yayin wani sintiri da dakarunta s**a gudanar.

Binciken da aka gudanar ya kai ga gano katin shaidar aikin soja na bogi, katunan ATM guda huɗu, gajeren wandon kayan sojoji, agogon hannu da kuma kuɗi Naira 17,000 a hannunsa k**ar yadda Gidan talavishion na TVC News s**a ruwaito.

Rundunar ta kumace an tsare wanda ake zargin tare da kayayyakin da aka ƙwace domin ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

05/07/2026

Labaran Duniya ..

05/07/2026

TAKAITATTUN LABARAI

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sabuwar muryar Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share