02/07/2026
Gwamnatin Tarayya Ta Samu Nasarar Hukuncin Dauri Ga ’Yan Ta’adda 1,721 Tun Daga 2017 – ONSA
Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (ONSA) ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta samu nasarar tabbatar da laifin ta’addanci ga mutum 1,721 tun bayan fara shirin shari’a kan masu laifukan ta’addanci a watan Oktoban shekarar 2017.
Daraktan Harkokin Shari’a na ONSA, Zakari Mijinyawa, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin taron haɗin gwiwa na masu magana da yawun hukumomin tsaro, soji da jami’an tabbatar da doka da oda a Abuja.
Ya ce shirin, wanda ONSA ke jagoranta tare da Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, bangaren shari’a da hukumomin tsaro, ya kammala matakai goma na gudanar da shari’o’in ta’addanci.
A cewarsa, an kuma sallami ko wanke waɗanda ba a samu isassun hujjojin da za su tabbatar da laifinsu ba, domin mutunta ƙa’idodin adalci da damar samun shari’a ta gaskiya.
Mijinyawa ya ce matakai uku na farko da aka gudanar tsakanin 2017 zuwa 2018 sun samar da hukunci kan mutum 366, an sallami mutum 882, an wanke mutum biyar, yayin da aka ɗage shari’ar mutum 61.
Ya ƙara da cewa matakai na huɗu zuwa na takwas, da aka gudanar tsakanin 2023 zuwa 2025, sun haifar da hukunci 490, ciki har da laifukan tallafa wa ta’addanci, manyan laifukan ƙasa da ƙasa da kuma laifukan cin zarafin mata da yara.
Hakazalika, matakai na tara da na goma da aka gudanar a shekarar 2026 sun samar da hukunci 865, adadin da ya zarce rabin dukkan hukuncin da aka samu tun bayan fara shirin.
Ya bayyana cewa wannan adadi na shekarar 2026 ya fi jimillar hukuncin 856 da aka samu a cikin shekaru tara da s**a gabata.
Mijinyawa ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na tabbatar da hukunta masu aikata laifukan ta’addanci tare da kiyaye kundin tsarin mulki da bin doka da oda.
Daga jaridar: Fitila Hausa News