
27/07/2025
Hausawa yau ta ke Ranar Al'adun Hausa ta Duniya 27 ga watan 7, Yuli
Yau ta ke Ranar Bikin Bajekolin Al'adun Hausa ta duniya, 27 ga watan 7, Yuli
Wannan rana ce da Hausawa a ko'ina a fadin sagagi su ke bajekolin al'adun su wanda sun ka hada da gine-gine, bukukuwa, harshen Hausa, masarautu, abunci, wakoki, tufafi, raye-raye, zamantakewa da dai sauran su.
Mu na maraba da wannan rana.
Daga ranar 9 zuwa 11 na watan Mayu shekarar 2025 an yi wani mahimmin taro a Jami'ar Joseph Ki-zerbo da ke Ouagadougou a kasar Burkinafaso inda Hausawa daga kasashe dabam-dabam sun ka tattauna makomar harshen Hausa, al'adu da rayuwar Hausawa a yau.
Taron na kwana uku mai take "Gudunmawar da harsunan kasa su ke bayarwa wajen samun yancin kai, kishin kasa, da tabbatar da zamanlafiya, masamman mayar da hankali kan harshen Hausa", masana sun gano ranar da ta fi cancanta ta zama Ranar Al'adun Hausawa da Harshen Hausa ita ce ranar 27 ga watan 7, Yuli.
Ku sani:
Kafin wannan taro wasu Fulani karkashin jagorancin Abubakar Mahmoud Gumi, Sanusi Lamido Sanusi, Sambo Dasuki sun yi niyyar ruguza mu da sun kirkiro ranar da ba ta dace da al'adun Hausa ba watau 26 ga watan August wajen shekara 40 da ta gabata wadda wani yaro Abdulbaki Jari ya ke tallatawa a kafofin sadarwa tun daga shekarar 2015. Mu Hausawa mun soke ranar 26 ga watan August a matsayin ranar Hausa domin ba ta yi daidai da ranar da Bahaushe ya ke bukukuwa ba. Hasalima ba a ranar harshe sai idan ba harshen Hausa, Fulani su ke son su sace ko garkuwa da shi ba. Ba a ma mai rai karya.
Sannan mu na gayyatar Hausawa maza da mata mu hadakai mu raya wannan rana 27 ga watan 7, Yuli domin a wannan ranar ce kakannin mu su ke bude daji, a wannan rana Sarakunan ruwa a KasarHausa su ke fadawa mutane da ke kusa da kogi su hau saman tudu idan za a yi ambaliyar ruwa. A wannan rana masanan ilimin yanayi su ke bincike koda za a yi iska su sanar cikin gaggawa a yi turi ko yabe a gidaje. A wannan rana masana su ke bincike su gano abunda damina za ta bada lokacin noma.
Mu na kiran Hausawa ko'ina a fadin duniya mu raya wannan rana domin rana ce ta alfahari. Mu na ma Allah godiya da zuwan wannan lokaci da Hausawa sun ka fara kirkiran abun kan su da kan su. Sannan mu na jinjina ga magabatan mu Kakannin mu Hausawa da sun ka gada ma mu abubuwan da mu jikoki za mu yi tunkaho da su.
Godiya ta masamman ga Hausawa da sun yi ta maza sun shirya wannan taro da ya zabi wannan rana "LE FORUM INTERNATIONAL DE LANGUE HAUSA (FILHA)" (The International Forum of the Hausa Language), wanda Majalisar Hausa ta Duniya (COMOHA) da Cibiyar Nazarin Harsunan Tarayyar Afirka (ACALAN-UA) tare da hadingwiwar kungiyar Hausawa ta kasa da kungiyar Makaranta sun ka shirya.
Kaltum Alumbe Jitami (Uwar Gwagwarmaya Kwatar Yancin Hausawa)
Watch video/post https://www.kasarhausa24.com/hausawa-yau-ta-ke-ranar-aladun-hausa-duniya-27-ga-watan-7-yuli/