18/09/2025
Yadda Kansila yayi amfani da Kwamishinan yan Sandan Jahar Katsina domin aika Dan Jarida Magarkama bayan fallasa zambar Miliyan 30.
A yau ne 18 ga watan 9, 2025 kotun majestire mai lamba biyu dake katsina ta aika da Editan jaridar Leadership Hausa Online News Ltd Zuhair Ali Ibrahim gidan yari bisa bukatar yan sanda na ajiye shi har sai an gama binciken wani korafin da kansilan Doro dake karamar hukumar Bindawa Abubakar Nuhu ya shigar akan sa.
Kansilan ya shigar da korafin ne, akan wani labari da Jaridar leadership Hausa Online ta rubuta a ranar 7 ga watan satumba inda wani mai suna Alhaji Ibrahim sa'adu yayi korafi da ikirarin kansilan Doro Abubakar Nuhu ya canye masa wasu kudin sa har naira milyan talatin. (30M)
A labarin da Jaridar ta buga tace Alhaji Ibrahim sa'adu ya bayyana cewa shi Ubangidan kansilan ne,kuma ya sha taimakonshi ya kuma yarda dashi amma yayi amfani da wannan yardar wajen damfarar shi kamar yadda yayi zargi.
Editan yayi kokarin jin ta bakin kansilan Abubakar Nuhu amma abin yaci tura don haka s**a buga labarinsu a bisa ana zargin kansilan Abubakar Nuhu .
Kansilan Abubakar Nuhu ya kai kara wajen yan sanda inda aka je har zaria aka kamo zuhair a ranar litinin din data gabata zuhair ya fada ma yan sanda duk yadda ya samu labarin shi da kokarin shi na jin ta bakin kansilan amma abin yaci tura.
Wasu mutane a katsina sunyi kokarin shiga maganar don dai daitawa amma kansilan ya rika Saba alkawalin da ya dauka na janye maganar da sasantawa.
Mutanen da s**a shiga maganar don sansantawa sune Mai ba Gwamnan Katsina Dr. Dikko Umaru Radda shawara akan harkokin jam'iyyu Alhaji shafi i Duwan, sai Dan majalisar tarayya mai wakiltar Mani da Bindawa, sai Alhaji yusufu Ibrahim jargaba sai kuma Malam Danjuma katsina .
Kansilan sai ya amsa za a dai daita amma kuma ya Saba alkawalin, Kansilan yana neman tozarta Editan na leadership online newspaper bisa wata bukatar kashin kanshi, ko kuma don ya tsorata marubuta su bar fallasa komai nashi.
Rariya Online