22/09/2025
TARON MATASAN ANGUWAN MADAKI DAKE NAN CIKIN GIRIN TUMU DOMIN NUNA GOYON BAYAN SU WAKILIN BIRNIN PINDIGA.
A yau ne al’ummar Anguwan Madaki Dake Nan cikin garin Tumu sun gudanar da taro mai tarihi tare da manyan masu ruwa da tsaki na Matasan anguwan, inda s**a hadu domin jaddada goyon bayansu ga (Wakilin Birnin Pindiga) Alh.Musa Baba Tumu a tunkarar takarar kujerar Dan Majalisar Jaha Na Gombe, 2027.
Wannan taro ya kasance wata shaida ta hadin kai, zumunci da kuma kwarin gwiwa da al’umma ke nunawa ga Hon.Musa Baba Tumu (Wakilin Birnin Pindiga) bisa irin jagoranci nagari, kishin kasa da kuma nagartar shugabanci daya dace ya jagoranci Al'ummar kasar Pindiga a 2027
Matasan anguwan Madaki Dake Nan cikin garin Tumu sun bayyana cewa lokaci yayi da jama’ar Kasar Pindiga zasu amfana da gogewa da hangen nesan na Hon.Musa Baba Tumu wanda ke da cikakken shiri da tsare-tsaren cigaban kasar Pindiga a fannoni daban-daban kamar ilimi, lafiya, noma, da bunkasa matasa, Mata da Dattawa.
Matasan anguwan Madaki Dake Nan cikin garin Tumu Sunce duk wannan gogewan da irin aikin alhairi da Wakilin Birnin Pindiga yakeyi a yankin kasar Pindiga Nan ya biyo bayan irin aikin alhairi da shi Jagoran Siyasar kasar Nan yakeyi Wato Mai girma Sanata Mohammed Danjuma Goje (Sarkin Yakin Gombe) ne duk Yana koyi ne da irin aiyukansa da yakeyi babu dare ba Rana a kasar Nan.
A karshen taron daukacin jama’ar Matasan anguwan Madaki Dake Nan cikin garin Tumu suna tare da shi a wannan tafiya ta Wakilin Birnin Pindiga kowa Namu Ne Birni da karkara wace za ta tabbatar da samun cigaba da walwala ga kowa da kowa a yanki Nan insha Allah
Kowa Namu Ne Birni da karkara Wakilin Birnin Pindiga Muke Fata insha Allah 2027.