KCB Hausa News

KCB Hausa News 𝐌𝐄𝐃𝐈𝐀

Tinubu zai samarwa Nijeriya cikakkiyar wutar lantarki nan da 2027 - Minista Ministan Wutar Lantarki ya ce ‘Yan Najeriya ...
05/08/2025

Tinubu zai samarwa Nijeriya cikakkiyar wutar lantarki nan da 2027 - Minista

Ministan Wutar Lantarki ya ce ‘Yan Najeriya za su more cikakkiyar wutar lantarki ba tare da yankewa ba kafin ƙarshen wa'adin farko na mulkin Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Yayin ƙaddamar da sabuwar tashar rarraba wuta ta Kwaru mai girman 1X15 MVA/ 33/11 kilovolt (KV) da ke unguwar Ikotun-Egbe a Legas, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana da cikakken ƙuduri na cika wannan buri kafin ƙarshen wa’adin mulkinsa na farko.

A wajen taron da aka gudanar a karshen mako, ministan ya ce shugaban ƙasa na ci gaba da ɗaukar matakai da dama don inganta samarwa da rarraba wutar lantarki a fadin ƙasar nan.

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Cewa Farashin Kayan Abinci Zai Ci Gaba Da Sauka — Jiragen Ruwa 35 Sun Nufi Na...
05/08/2025

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Cewa Farashin Kayan Abinci Zai Ci Gaba Da Sauka — Jiragen Ruwa 35 Sun Nufi Najeriya Dauke da Kayan Abinci da Man Fetir

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na ɗaukar matakan rage tsadar kayan abinci a ƙasar, tare da gargaɗin ’yan kasuwa da ke ɓoye kaya don haifar da ƙarin tsada, cewa wannan dabarar ta kare – domin kuwa farashin kayan zai cigaba da faɗuwa, wanda hakan zai jefa su cikin asara.

A cewar sanarwar, gwamnati ta ce tuni jiragen ruwa guda talatin da biyar (35) s**a nufo Najeriya dauke da nau’ikan kaya da s**a haɗa da tataccen man fetur, abinci, da kayayyakin masarufi, inda za su sauka a manyan tashoshin jiragen ruwa na jihar Legas: Apapa da Tin Can Island.

Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA) ta bayyana cewa daga cikin waɗannan jirage 35, guda 14 na ɗauke da tataccen man fetir, yayin da sauran 21 ke makare da kaya irin su:

Danyen kifi

Accha

Kayan ƙarafa

Siga

Manja

Taki

Man gas

Da sundukai masu ɗauke da kayan masarufi daban-daban.

Baya ga waɗannan, NPA ta kara da cewa akwai wasu jirage guda 11 da tuni sun iso tashoshin Najeriya, suna jiran sauke kayan da s**a haɗa da taki, mai, da wasu muhimman kayayyaki.

Gwamnati ta jaddada cewa wannan mataki wani bangare ne na kokarin da take yi don saukaka rayuwar al’umma, rage hauhawar farashi, da kuma dakile ayyukan ’yan kasuwa masu son tattara kaya don hana jama’a su samu cikin sauƙi.

ABIN FARIN CIKI: Ya Je Tambayar Maigidansa Kudin Da Zai K**a Haya Saboda Aurensa Ya Gabato, Kawai Sai Maigidan Nasa Ya M...
11/07/2025

ABIN FARIN CIKI: Ya Je Tambayar Maigidansa Kudin Da Zai K**a Haya Saboda Aurensa Ya Gabato, Kawai Sai Maigidan Nasa Ya Mika Masa Takardar Gidan Da Ya Siya Masa Kyauta

Bikin abokina Abdul Ɗorayi za a yi saura sati hudu, sai ɗazu muka je gidan me gidansa domin maganar kuɗin hayar gidan da za su zauna.

Abin mamaki Wallahi sai maigidan nasa ya ce yana zuwa, muna nan zaune a ƙofar gidansa kawai sai gashi da takardar gida ashe ya siya masa gida, Wallahi tsabar daɗi ni da shi kawai sai ga hawaye a idanunmu.

Muka kira babarsa a waya muka gaya mata kawai sai ta saki wayar ta faɗi ta fashe tana kukan daɗi.

Ya Rabbi Ka sanya albarka, Ka biyawa Ogan nasa da gidan Aljannah.

Wannan shine cikakken uban gida.

Daga Comr Bashir Isiyaku Gaida

Gwamna Abiodun ya baiwa iyalan ƴan wasan Kano da su ka rasu a hatsarin mota Naira Miliyan 31Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abi...
02/06/2025

Gwamna Abiodun ya baiwa iyalan ƴan wasan Kano da su ka rasu a hatsarin mota Naira Miliyan 31

Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, a ranar Lahadi ya aike da tawaga zuwa Jihar Kano domin yi wa gwamnatin jihar da al’ummar Kano ta’aziyya bisa rashin wasu 'yan wasa da jami'ai da s**a rasu yayin dawowa daga gasar wasanni ta kasa da aka kammala kwanan nan.

Gwamna Abiodun ya kuma ba da gudummawar Naira miliyan daya (N1m) ga kowanne iyali daga cikin iyalan mamatan a matsayin taimako na farko, wanda jimillar kudin ta kai Naira miliyan 31.

A cewar wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, mataimakiyar gwamna, Injiniya Noimot Salako-Oyedele ce ta jagoranci tawagar, da ta haɗa da Sakataren Gwamnatin Jihar Ogun, Mista Tokunbo Talabi; Kwamishinan Ci gaban Wasanni, Hon. Wasiu Isiaka; da Sakataren Gudanarwa na Kwamitin Shirya Gasar wasanni ta kasa Dr. Kweku Tandoh.

Tawagar ta iso Kano da misalin ƙarfe 9 na safe, inda mataimakin gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdusalam Gwarzo, tare da wasu jami'an gwamnatin Kano s**a tarbe su.

Yayin da ta ke bayyana jimamin Gwamna Abiodun kan wannan musiba, Salako-Oyedele ta miƙa sakon ta’aziyya ga gwamnatin Jihar Kano.

Ta ce:"Mun san cewa gwamnan yana wajen aikin Hajji a yanzu, amma mun ga ya dace mu zo da kanmu domin nuna goyon bayanmu ga Gwamna, Gwamnati da al’ummar Jihar Kano a wannan lokaci na jarrabawa.

"Wannan babban rashin da ya shafi Jihar Kano ne, masu ruwa da tsaki a fannin wasanni gaba ɗaya, musamman dangin mamatan da abokan arzikinsu. Muna kuma addu'ar Allah ya ba wa waɗanda ke kwance a asibiti lafiya cikin gaggawa.

YANZU-YANZU: Hukumar tace finai finai ta jihar Kano ta dakatar da nuna fim din 'Labarina' da gidan Sarauta da wasu karin...
19/05/2025

YANZU-YANZU: Hukumar tace finai finai ta jihar Kano ta dakatar da nuna fim din 'Labarina' da gidan Sarauta da wasu karin fina finai 20

A kokarinta na tabbatar da ana bin dokar tace fina-finai sauda kafa tare da kara dora masana'antar kannywood a kan saiti, Hukumar tace fina-finai da Dab'i ta Jahar Kano karkashin jagorancin Alh Abba El-mustapha ta dauki wani gagarun mataki domin tsaftace yadda ake sakin fina-finai barkatai batare da cika ka'idar da doka ta tanadar musu ba na kawo kowanne film gabanta a tantance shi kafin ya isa ga idanun al'umma inda ta dakatar da wasu Manyan Fina-finai har guda 22 daga sakasu a kafafen Internet ko gidan TV

Abba El-mustapha ne ya bayyana wannan mataki biyo bayan tattaunawa da manyan jami'an Hukumar tare da dogon nazari domin kawo karshen korafe korafen da Hukumar take yawan karba dan kara inganta aiyukan Hukumar tare da masana'antar kannywood.

Abdullahi Sani Sulaiman shine jami'in yada labaran Hukumar ya bayyana fina-finai da aka dakatar kamar haka:

1. Dakin Amarya
2. Mashahuri
3. Gidan Sarauta
4. Wasiyya
5. Tawakkaltu
6. Mijina
7. Wani Zamani
8. Labarina
9. Mallaka
10. Kudin Ruwa
11. Boka Ko Malam
12. Wa yasan Gobe
13. Rana Dubu
14. Manyan Mata
15. Fatake
16. Gwarwashi
17. Jamilun Jiddan
18. Shahadar Nabila
19. Dadin Kowa
20. Tabarma
21. Kishiyata
22. Rigar Aro

Ya kara da cewa doka ce ta bawa Hukumar damar tace duk wani film tare da lura da aiyukan ‘yan masana'antar kannywood matsawar suna da rejista da Hukumar a ko ina suke, A saboda haka ana shawartar masu daukar nauyin wannan fina-finai da su tabbatar da sunbi wannan doka ta dakatarwa tare da tsayar da saka wannan fina-finai a gidajen TV ko kafar internet. Haka kuma ana sanardasu cewa su miko fina-finansu ga Hukumar domin tantance su tare da basu shaidar inganci ta tacewa nanda sati daya mai zuwa wato daga *LITININ, 19 ga watan MAYU, 2025 zuwa 25 ga MAYU, 2025* domin gujewa fushin doka.

A karshe Hukumar ta nemi hadinkan dukkannin gid

CIKIYA CIKIYA CIKIYA Muna kira ga al’umma da su taya mu da addu’a ga ɗan’uwanmu, Baba Azare, wanda aka neme shi aka rasa...
14/05/2025

CIKIYA CIKIYA CIKIYA

Muna kira ga al’umma da su taya mu da addu’a ga ɗan’uwanmu, Baba Azare, wanda aka neme shi aka rasa tun jiya da misalin ƙarfe goma na safe wayoyin sa a kashe.

Rahotanni sun nuna cewa zuwa yanzu ba mu da tabbacin lafiyarsa ko inda yake, lamarin da ya ɗaga hankalin dangi, abokai da al’umma gaba ɗaya.

Don haka, muna roƙon ku da ku tayamu da addu’a da fatan Allah Ya dawo mana da Baba Azare cikin koshin lafiya, Ya kare shi daga sharri, Ya kuma ba mu cikakken haske game da halin da yake ciki.

Daga. Abbati Mohammed

Address

Kano, Road Azare, Bauchi, State
Katagum

Telephone

+2347067658337

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when KCB Hausa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share