05/08/2025
Wasu hazikan Yara Yan Makarantar Sakandire su Biyu sun dauki babbar lambar Yabo a gasar duniya da ta Gudana a Birnin London na gasar harshen turanci sun dauki na Farko, nafisa Abdullahi, da Rukayya Fema. Kuma dalibai ne a NTIC Yobe.
____Comrd.Yakubu Mukhtar Ibrahim Nguru.
Nan take Mai Girma Gwamnan jihar Yobe Hon. (Dr) Mai Mala Buni CON, COMN, ya amince da wani gagarumin biki na karrama Nafisa Abdullah mai shekaru 17 da Rukayya Muhammad Fema mai shekaru 15 a matsayin gwarazan duniya a fannin fasahar harshen Ingilishi da gasa baki daya a gasar cin kofin duniya na TeenEagle na shekarar 2025 a birnin Landan na kasar Birtaniya.
Nafisa da Rukayya ‘yan jihar Yobe daliban ne na Kwalejin Tulip International ta Najeriya, wadanda s**a wakilci Najeriya a gasar ta duniya inda s**a doke sauran mahalarta 20,000 daga kasashe 69.
Nafisa da Rukayya dukkansu sun ci gajiyar shirin tallafin karatu na Gwamna Mai Mala Buni wanda ya kunshi cikakken karatun dalibai 890 a kwalejin Najeriya Tulip International College.
Mai Girma Gwamna Buni' ya bayyana rawar da s**a taka a matsayin babban abin alfahari ga jiha da kasa. Kuma yanuna Farin cikinsa kasancewar wannan yaran Yan asalin Jihar Yobe ne. Inda yace lalle Yayi alfahari da hakan, Kuma wazibi a karramasu a Jiharsu.
“Wadannan manyan ayyuka ne da ke sa mu yi alfahari da kuma tabbatar da saka hannun jarin da gwamnati ke yi a fannin ilimi,” in ji Gwamna Buni.
"Mai Girma Gwamna Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bayar da tallafin karatu ga kowane yaro a jihar domin samun damar zuwa makaranta, ya kuma yi kira ga iyaye da su ba su hadin kai.
Kuma Gwamnati ta sake gina makarantun da ‘yan ta’addan s**a lalata, tare da samar da kayayyakin daki, litattafai, kayan aikin dakin gwaje-gwaje da kuma samar da kwararrun malamai domin inganta harkar ilimi a jihar, kuma har yanzu aikin na kan gaba.
A halin yanzu, akwai kimanin daliban jihar Yobe 40,000 da ke samun tallafin karatu na gwamnati da ke karatun kwasa-kwasai daban-daban a Jami’o’i da sauran manyan makarantu a Najeriya da kasashen ketare.
Idan bamu manta ba a ‘yan watannin da s**a gabata jihar ta yi bikin yaye dalibai 167 da s**a ci gajiyar shirin tallafin karatu da jihar ta samu wadanda s**a kammala karatunsu a fannin kimiyyar likitanci da na’ura mai kwakwalwa da injiniyanci daga jami’o’in Indiya.
Insha Allah Muna fatan wata shekara ma Yobe zata dauki ta daya a wannan gasar. Gwamna Yayi alkawarin yimusu gagarumin kyauta Ga wayenan yaran su Biyu.
Yakubu Mukhtar Ibrahim nguru.