Starlighte Tv

Starlighte Tv Anbude wannan shafin na stalighteTv a ranar 18-2-2019 domin kawomuku ingantattun labarai domin karin bayani a tuntubemu ta wannan lamba 08126299115

01/06/2026

Tsohon mataimakin gwamnan kano kuma dan takarar gwamna a Jam'iyyar NDC kwankwassiyya Comr. Aminu Abdussalmu gwarzo ya mayarwa da gwamna Abba kabir yusif martani.

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya mayar da martani mai daukar hankali ga t...
29/05/2026

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya mayar da martani mai daukar hankali ga tsohon ubangidansa a siyasa, Rabiu Musa Kwankwaso, inda ya ce shi ma Kwankwaso “ya taba zama yaro” a siyasarsa.

Kalamin Ganduje na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takun-saka tsakanin manyan jagororin siyasar Kano kan batun karfin iko da tasiri a siyasa gabanin zabukan 2027.

Ganduje ya tuna da zaben fidda gwani na gwamna a shekarar 1998, inda ya ce mutane da dama sun san cewa shi ne ya yi nasara, amma dattawan siyasa s**a roke shi da ya hakura domin samar da hadin kai, lamarin da ya sa ya amince ya zama mataimakin dan takarar gwamna tare da Kwankwaso.

A cewarsa, duk da wannan mataki, sun yi aiki tare cikin fahimta da nasara daga 1999 zuwa 2003, sannan daga 2011 zuwa 2015, inda s**a jagoranci harkokin siyasar Kano a matsayin manyan abokan siyasa.

Sai dai dangantakar tasu daga baya ta rikide zuwa gasa mai zafi bayan rabuwar kai a siyasance, lamarin da ya haddasa rikice-rikice da rabuwar magoya baya zuwa bangarori biyu a Kano.

Masu sharhi na ganin wannan sabon furuci na Ganduje wani sabon salo ne na nuna cewa shi ma yana da tarihi da tasiri kafin fitowar Kwankwasiyya.

Yayin da magoya bayan bangarorin biyu ke cigaba da musayar kalamai a kafafen sada zumunta, mutane da dama na ganin siyasar Kano na kara daukar sabon salo gabanin babban zaben 2027.

Sai dai tambayar da mutane da yawa ke yi yanzu ita ce: Shin wannan musayar kalamai za ta kara dagula siyasar Kano, ko kuwa wata alama ce ta sabon rikicin neman karfin iko tsakanin tsoffin abokan tafiya?
#

Tsohon gwamnan kano Engr. Rabiu musa kwankwaso ya tsayar da Comr. Aminu Abdussalmu gwarzo a matsayin dan takarar gwamna ...
29/05/2026

Tsohon gwamnan kano Engr. Rabiu musa kwankwaso ya tsayar da Comr. Aminu Abdussalmu gwarzo a matsayin dan takarar gwamna a Jam'iyyar NDC kwankwassiyya wanda haka ke nuna gwarzo zai fafata da gwamna Abba kabir yusif wanda yayiwa mataimaki a zaben 2023

Wa kukewa fatan nasara?

Tashar Channel 12 Israel ta rawaito cewa firaministan Israel, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa ya umarci sojojin ƙasa...
29/05/2026

Tashar Channel 12 Israel ta rawaito cewa firaministan Israel, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa ya umarci sojojin ƙasar su ƙwace iko da kashi 70 cikin 100 na yankin Gaza Strip.

Rahoton ya ce Netanyahu ya bayyana hakan ne yayin wani taro a wani matsugunin Yahudawa da ke yankin West Bank da Isra’ila ta mamaye.

“Yanzu muna matsa wa Hamas lamba. Muna iko da kashi 60 cikin 100 na yankin Gaza. Mun tashi daga kashi 50 zuwa 60, kuma umarnina shi ne mu kai zuwa kashi 70,” in ji shi kamar yadda bidiyon da tashar ta wallafa ya nuna.

Kalaman nasa na zuwa ne duk da yarjejeniyar tsagaita wuta mai rauni da aka ce ta fara aiki tun watan Oktoba.

Jam'iyyar APC ta tsayar da Mal. Ibrahim Shekaru a takarar sanatan kano central yayin da Jam'iyyar NDC kwankwassiyya ta t...
29/05/2026

Jam'iyyar APC ta tsayar da Mal. Ibrahim Shekaru a takarar sanatan kano central yayin da Jam'iyyar NDC kwankwassiyya ta tsayar da Dr. Nasiru Yusif Gawuna.

Wa kuke ganin zaiyi nasara Uban gida ko yaronsa?

Kwankwaso ya mayarwa da gwamna Abba kabir yusif martani kan cewa Abba yace shi ba yaronsa bane, inda Engr. Rabiu musa kw...
28/05/2026

Kwankwaso ya mayarwa da gwamna Abba kabir yusif martani kan cewa Abba yace shi ba yaronsa bane, inda Engr. Rabiu musa kwankwaso yayi zazzafan martani harma yace ko Ganduje be isa yace ba yaronsa bane a siyasa.

Me zaku ce?

26/05/2026

Tsohuwar ajjiya

Yanda aka Sha fama da Obasonjo kafin kaddamar da shari'ar musulunci a Najeriya

Innalillahi wa'inna illahirraju'un Allah yayiwa (Dr.) Mahmud Baffa Yola rasuwa bayan fama da jinya kafin rasuwarsa ya ri...
25/05/2026

Innalillahi wa'inna illahirraju'un Allah yayiwa (Dr.) Mahmud Baffa Yola rasuwa bayan fama da jinya kafin rasuwarsa ya rike mukamai daban daban cikin harda Comissioner for Water Resources and Rurul Development, yabar mata,Yaya da kuma jikoki muna addu'a Allah ya gafarta masa.

Spain ta saka Lamin Yamal cikin tawagar 'yan wasanta da zasu je gasar kofin Duniya duk da rauni da yake fama da shiKocin...
25/05/2026

Spain ta saka Lamin Yamal cikin tawagar 'yan wasanta da zasu je gasar kofin Duniya duk da rauni da yake fama da shi

Kocin tawagar ƙasar Spain, Luis de la Fuente, ya saka matashin ɗan wasa Lamine Yamal cikin jerin ‘yan wasan da za su wakilci ƙasar a gasar Kofin Duniya ta 2026 duk da rahotannin cewa yana fama da rauni.

Rahotanni sun bayyana cewa Yamal ya samu matsalar rauni a baya-bayan nan, lamarin da ya janyo damuwa tsakanin magoya baya da masu bibiyar ƙwallon ƙafa kan ko zai samu lafiya kafin fara gasar.

Sai dai kocin Spain ɗin ya nuna amincewa da yanayin lafiyar ɗan wasan, yana mai cewa an saka shi cikin tawagar ne bayan amincewar likitoci da jami’an lafiya na ƙungiyar.

NDC za ta kaddamar da kwamitin tantance ‘yan takaraTsohon gwamnan jihar Bayelsa kuma jagoran jam’iyyar NDC, Sanata Seria...
25/05/2026

NDC za ta kaddamar da kwamitin tantance ‘yan takara

Tsohon gwamnan jihar Bayelsa kuma jagoran jam’iyyar NDC, Sanata Seriake Dickson, zai kaddamar da kwamitin tantance ‘yan takara mai mutum 21 a ranar Litinin a Abuja, a wani bangare na shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027.

A wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam’iyyar, Osa Director, ya fitar, ya ce an kafa kwamitin ne bayan kammala tantance masu neman takarar gwamna, ‘yan majalisar dokoki ta kasa da kuma na jihohi a fadin Nijeriya.

Sanarwar ta bayyana cewa an kafa kwamitin ne domin tabbatar da adalci a cikin harkokin cikin gida na jam’iyyar, tare da duba rahotannin da kwamitocin tantance ‘yan takara s**a gabatar daga jihohi daban-daban.

Address

Katampe Ext

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Starlighte Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share