
31/07/2025
An Karrama Tsohon Baturen ’Yan Sanda da Marigayi ASP Sale Ya’u a Dandume
A ranar Alhamis, 31 ga Yuli, 2052, an gudanar da bikin karrama tsohon Baturen ’yan sanda na karamar hukumar Dandume, CSP Emmanuel Zangina, da marigayi ASP Sale Ya’u, tsohon jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sanda a yankin.
Bikin ya gudana ne a harabar sakatariyar karamar hukumar Dandume, karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar, Hon. Bashir Sabi’u Musa (Gyazama), tare da hadin gwiwar kwamitin tsaron garin Dandume.
An karrama CSP Emmanuel Zangina ne bisa jajircewarsa da kwarewa a aiki, da kuma karin girma da aka yi masa tare da sauya masa wurin aiki zuwa Shaidam a jihar Filato.
A yayin taron, mahalarta sun bayyana CSP Zangina da marigayi ASP Sale Ya’u a matsayin jaruman da s**a nuna kwazo da sadaukarwa a lokacin da suke bakin aiki, musamman wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Shugaban karamar hukumar, Hon. Bashir Sabi’u Musa, ya ce tun bayan tafiyar CSP Zangina, an nada CSP Muhammad Haruna Uba a matsayin sabon baturen ’yan sanda a Dandume. Ya ce sabon baturen ya riga ya fara daukar matakai na gyaran motocin sintiri da karfafa tsaro domin tunkarar hare-haren ’yan bindiga a yankin.
Ya kuma bukaci kwamitin tsaron gari da ya fadada ayyukansa zuwa dukkan gundumomi 11 da ke cikin karamar hukumar domin tabbatar da tsaro mai dorewa.
Mai martaba Hakimin Dandume, Alhaji Ja’afar Ibrahim Sambo, wanda ya samu wakilcin Alhaji Shamsuddeen Ja’afar Ibrahim, ya yaba da aikin CSP Zangina tare da kiraye-kirayen da sabon baturen ya ci gaba da jajircewa wajen kare lafiyar al’umma.
Kwamitin tsaron Dandume ya yi amfani da damar wajen bayyana wasu daga cikin nasarorin da s**a samu da kalubalen da suke fuskanta, tare da roƙon gwamnatin da al’umma da su ci gaba da bayar da goyon baya ga jami’an tsaro.
Abokan aikin marigayi ASP Sale Ya’u da wasu daga cikin al’ummar Dandume sun bayyana irin kishin kasa da sadaukarwar da ya nuna, tare da cewa ya rasu ne yayin da yake kokarin dakile harin ’yan bindiga a kan hanyar Magaji Wando a bara.
Taron ya samu halartar manyan baki da s**a hada da sarakuna, shugabannin al’umma, ’yan kasuwa, wakilan kungiyoyi, mata, matasa, da ’yan uwa da abokan arziki. An rufe taron da addu’o’in zaman lafiya da fatan alheri ga yankin karamar hukumar Dandume.