Al'Irfan

Al'Irfan Ya Ubangiji! Kai kake jujjuya zukata, Ya Allah! Ka tabbatar da zukatanmu akan addininka.

20/09/2025

Indai kana da hali (ka mallaki miliyan biyar zuwa sama) Wallahi kawai kaje ka nemi lasisi ka mallaki makami, domin magani irin waɗannan miyagu. Kana zaune gida wani ya zo ya yi maka wulakanci a cikin iyalinka.

17/09/2025

Al'ada tana da daɗi da burgewa

15/09/2025
15/09/2025
13/09/2025
12/09/2025

Gwamna mai jin ƙai da tausayin al'ummar shi!

Shekaru da dama a baya ya san shi, kwatsam jiya sai ya hango shi a wajen taro, nan take ya nuna ma Orderly inda ya ganshi aka kira shi, kuma a nan take ya share mashi hawayen shi.

Allah ya ƙara jagora Malam Dikko Umaru Radda.

Dikko Radda

Duk wanda s**a Zaɓi Hon. Majigiri da kyakkyawar manufar yin ayyukan al'umma, ba domin wani dalili na ƙashin kaiba, suna ...
29/09/2024

Duk wanda s**a Zaɓi Hon. Majigiri da kyakkyawar manufar yin ayyukan al'umma, ba domin wani dalili na ƙashin kaiba, suna tare dashi! Kuma sunsan yana yin abunda aka zaɓe shi domin shi. Amma wanda ya zaɓe shi da manufar ɗora masa lalurar kai da kai, dole yaga gazawarsa, domin Hon. Majigiri na kowane.

Sannan muna da yaƙinin masu kushe shi, suna yi ne domin ganin yana yin wani abu na kyautatawa al'umma! Domin bashi kaɗai ba ne shugaba, hada wanda ko ganinsu ba'a yi. Amma ba'a damu dasu ba, domin kowa yasan basayin komai.

Insha Allahu ko da masu adawa na gida da na waje basu ƙauna, Mashi/Dutsi za a cigaba da yin abunda ya kamata.

Allah ya ƙara dafa maka Uban Hassan da Husaini🙏

SHUGABA...Da damar Shuwagabanin mu wanda Allah yaba dama ta shugabantar al'umma ko wakiltar su basu san ya za su jawo al...
08/08/2024

SHUGABA...

Da damar Shuwagabanin mu wanda Allah yaba dama ta shugabantar al'umma ko wakiltar su basu san ya za su jawo al'ummar su ba a jikin su wanda hakan zai saka wa Talakawan su ƙaunar su da yi masu addu'a.

Ba wai iya zuwa majalisa ka ɗaga hannu ba ne a matsayin ka na Wakilin al'umma don kai koken al'ummar ka game da neman biya masu wata buƙata. Wanda bai zama dole ba don ka kai wannan ƙudurin na al'ummar ka a zauren majalisa ace an cika maka shi.

Wannan ne yasa Hon. Salisu Yusuf Majigiri ya zama zakaran gwaji a cikin sauran takwarorin shi. Dalili kuwa Hon. Majigiri ya kasance Shugaba, kuma wakili wanda a koda yaushe saurare da jin matsalolin al'ummar shi su ne a gaban shi.

Ana son shugaba wanda baida ƙyamar al'umma, wanda yake shiga cikin lamuran al'ummar shi, wanda yake sauraren koken al'ummar shi, wanda yake jawo al'ummar shi a jikin shi, wanda damuwar al'ummar shi take zama damuwar shi. Duka waɗannan abubuwan da na lissafo Hon. Majigiri ya kasance Jajirtacce akan su.

Tabbas samun shugaba irin Hon. Majigiri ba ƙaramar nasara ba ce a cikin al'umma. Dole ne ko wace irin al'umma ta yi kwaɗayin samun irin shi a tare da ita.

Muna roƙon Allah S.W.T ya ƙara yi maka Jagoranci na alkairi wajen tafiyar da dukkan shuwagabancin Ka🤲

MAJIGIRI MEDIA TEAM💪
08/08/2024

MAJIGIRI YA HALARCI ZAMAN DA GWAMNAN JIHAR KATSINA YAYI DA ƳAN MAJALISAR TARAYYA NA JIHAR KATSINA SU 15:A ranar Juma'ar ...
02/06/2024

MAJIGIRI YA HALARCI ZAMAN DA GWAMNAN JIHAR KATSINA YAYI DA ƳAN MAJALISAR TARAYYA NA JIHAR KATSINA SU 15:

A ranar Juma'ar da ta gabata, Hon. Salisu Yusuf Majigiri (Garkuwan Gabas ɗin Katsina), wanda ya kasance ɗaya daga cikin ƴan majalisar wakilai 15 daga jihar Katsina wanda ke wakiltar ƙananan hukumomin Mashi da Dutsi a ƙarƙashin Jam'iyyar PDP.

Ya halarci zaman da Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda PhD yayi da dukkan ƴan majalissar tarayyar na jihar game da matsalar tsaro da jihar ta Katsina ke fuskanta.

Zaman ya samu halartar ƴan majalisar tarayyar su 15, inda s**a tattauna da kuma bada shawarwari tare da bada haɗin kai domin ganin an magance matsalolin tsaron da ya addabi jihar Katsina.

Anyi zaman a gidan Gwamnatin jihar Katsina da ke birnin tarayya Abuja, a ranar juma'ar da ta gabata 31/05/2024.

Allah yasa wannan zama ya kasance silar samuwar zaman lafiya a jihar mu ta Katsina da ƙasa baki ɗaya. Ameen🤲

MAJIGIRI MEDIA TEAM 💪
02/06/2024.

Address

Katsina Ala

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al'Irfan posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Al'Irfan:

Share