02/12/2024
Imaginary enemies.
A shekarar 2003 lokacin da muka koma wata unguwa daga cikin abokan da na fara haɗuwa da su akwai wani wanda kullum idan muka zauna hirarsa ɗaya ce; maƙiya sun yi masa yawa.
Irin gardawan nan ne waɗanda sun yi amanna da tasirin laƙani. Idan ya yi surƙullensa ko a mafarki ya ga kun yi rigima to ku na haɗuwa zai sauya maka fuska. Tun abin na ba ni mamaki har ya koma ba ni tsoro. Cikin ƙanƙanin lokaci duk mutanen da na san shi tare da su yace min maƙiyansa ne, amma a zahiri bai taɓa faɗa min wani abu da ɗayansu ya yi masa wanda zai tabbatar da ikirarinsa ba. Duk maƙiya ne waɗanda ya ƙirƙire su a tunaninsa. Wato imaginary enemies.
Watarana har gida ya zo ya same ni yace ya ga wani sabon maƙiyin a mafarki, amma dai bai gane kamanninsa sosai ba. Sai dai zai yi ƙoƙari ya gano ko wane ne.
Bayan kwana biyu ya daina zuwa inda nake. Mu na haɗuwa na yi masa sallama ya kawar da kai ya wuce batare da ya kula ni ba. Sai a lokacin na fahimci sabon maƙiyin da ya gano. Yarima ne.
Na gaskata abinda na yi zargi bayan da ya samu ƙanina yake yi masa ƙorafin cewa wai har da ni a masu yi masa asiri.
Sigmund Freud (1856-1939) a cikin aikinsa na psychoanalytic theory ya yi bayani kan abinda ya kira da 'paranoid delusion' yanayin da mutum zai yi ta hasashen wata masifa za ta same shi ko ana shirya masa wata manaƙisa daga maƙiyan da babu su a zahiri sai dai a tunani kawai.
Ka ga wannan wata rashin lafiya ce da ke damun mutane. Wataƙila ta wannan abokin nawa ta yi ƙarfin da ya dace ace an ga likita. To amma bari na ɗan ƙara bayar da misalai a taƙaice ta yadda za mu fahimci yadda imaginary enemies ke da tasiri a tunaninmu ta fuskoki daban-daban.
Wani duk lokacin da al'amura s**a rikice masa zai ce hannu aka sa masa. Idan ba ta samu miji da wuri ba, to wani ne ya yi mata asiri. Sun samu matsala da mai gidansa kan rashin fita wajen aiki da wuri, amma da za ku yi hira sai yace maka uban gidan hassada yake yi masa. Wani idan har ba abinda yake son ji kake faɗa masa ba, to kana cikin layin maƙiya. Ko ra'ayi ne na siyasa ya bambanta; to zai ja maka layi ya fara kallonka a matsayin maƙiyi.
Wani abin takaicin wasu daga gida ake fara dasa musu wannan tunanin tun suna ƙanana. Don za a yi ta yi musu bayanin cewa kawu wa ne da anti wance ba sa ƙaunar iyayenku don haka kun ga kuma ba za su so ku ba. Sai ka ga yaro ya taso yana yiwa 'yan uwan iyayensa kallon maƙiya alhali a zahiri ba maƙiyansa ba ne. Wataƙila kawai dai suna da wani saɓani ne ta fahimtar wasu al'amuran da iyayensa.
Bari mu kalli imaginary enemies ta wata fuskar amma kuma duk su na bayar da sakamako iri ɗaya.
Wani psychactrist kuma psychoanalyst mai suna Vamik Volkan ya yi bayanin imaginary enemies ta mahangar organizational psychology da kuma international relations. Ya yi rubutu kan yadda ta hanyar propaganda da watsa bayanan ƙarya ake ƙirƙirarwa da al'umma gabaɗaya imaginary enemies.
Idan kai matashi ne ɗan ƙabilar Ibo wanda bai karanta tarihin yaƙin basasan da aka yi a nan ƙasar ba. Sai ka ci karo da littafin Chinue Achebe mai suna 'There was a country' Tun kafin ka gama karanta littafin za ka ji ka tsani Hausa Fulani Saboda yadda marubucin ya nuna cewa kusan gabaɗaya yaƙin an tsara shi ne don a kawar da al'ummar Ibo daga doron ƙasa.
Wannan misali ɗaya ne ta hanyar da ake ɗurawa al'umma dafi su kwankwaɗi tarihi a baibai har su ji cewa tabbas al'umma kaza ko yare kaza maƙiyansu ne na har abada. Wato imaginary enemies in collective form.
A yanzu haka da nake wannan rubutun ina kan hanyar zuwa garin Dutse da ke jahar Jigawa. Wasu mata biyu na hira sai na ji ɗayar ta ƙara min point batare da ta sani ba.
"Kin san dangin miji ba abin yarda ba ne..."
Wannan mu ma na cikin irin misalan yadda muke ƙirƙirarwa kan mu imaginary enemies. Tun kafin yarinya ta yi aure ta daɗe da jin wannan falsafar na cewa dangin miji maƙiya ne. Matsalar ita ce; ko da a zahiri ta samu dangin mijin mutanen kirki, yarda da waccan falsafar sai ya sa ta ke ganin al'amura a baibai. Ko wani laifi ta aikata idan yayar miji ta yi mata faɗa sai ta ke kallon abin a matsayin ƙiyayya ce irin ta dangin miji.
A taƙaice za mu iya kasa falsafar imaginary enemies zuwa kamar haka:
1) Wasu maƙiyan kwata-kwata babu su a zahiri. Rikicewar tunani ne kawai ke haddasawa. Kamar dai abokina wanda na yiwa asiri.
2) Wata masifar da kake tunanin za ta same ka wataƙila har ka mutu ba za ta same ka ba. Kawai hasashe ne.
3) A wasu lokuta da gangan ake jirkita tarihi don kawai a samar wa mutane imaginary enemies.
4) Wani ba maƙiyi ba ne, ra'ayinku ne kawai ba iri ɗaya ba.
Matsalar farko ce kaɗai ke buƙatar ganin likita cikin gaggawa, amma sauran matsalolin duk za ka iya magance su ta hanyar nazari da bincike da koyon hangen al'amura ta fuskoki daban-daban. Iya tuhumar kai tare da koyawa kai cire son zuciya. Sannan kuma ma dai wa ya damu da kai ne?
Ni dai na san nawa, amma kai who is your imaginary enemy?
- Abdullahi Hassan Yarima