06/03/2023
AKWAI MATSALA BABBA
Wasu bayanan sirri ne na karanta akan wani shiri ta karkashin kasa da mutanen Peter Obi suke tsarawa
Zasu kaddamar da wani gagarumin zanga-zanga ne na lumana wanda zai dakatar da komai a cikin Kasarmu Nigeria, amma ta iya kasancewa ya rikide zuwa na tashin hankali
Mutanen Peter Obi sunce sune sukaci zaben Shugaban Kasa da ya gudana amma aka murde, suna ganin da zanga-zanga ne zasu kwaci hakkin su
Tabbas mutanen Peter Obi suna da tasirin da zasu iya dakatar da gudanuwar al'amura a cikin Kasarmu Nigeria
Bari na baku musali, manyan bankunan Nigeria na su ne, 75 na arzikin dake birnin tarayya nasu ne, karfin tattalin arzikin Nigeria yana hannunsu, idan sukace sun dakata zasu fita zanga-zanga to abin zai shafe mu sosai
Amma tabbas suna shirin zanga-zanga da zai girgiza Kasarnan, idan bukatarsu na kwatar mulki bai cika ba to zasu nemi a raba Kasar, shine ajandarsu na biyu a bayanan sirrin da na karanta
Don haka mu yi addu'ah, a matsayin mu na Musulmai kar mu yadda da zanga-zanga, domin baya cikin Karantarwan addinin mu
Allah Ya sa mu wanye lafiya.
Kukan Kurciya