12/01/2025
Duk jihar Katsina babu inda sunan Hamza Sule Wamban Faskari bai kai ba ta fuskar taimakon Al'umma.
Inji Hon. Haruna Abdulrashid Yaro Funtua Darakta Janaral na kungiyar Wamban Faskari Awareness Forum.
Hon. Haruna Abdulrashid Yaro ya fadi haka ne ranar lahadi 12-01-2024 lokacin da yake kaddamar da shugabannin kungiyar Wamban Faskari Political Awareness Forum na shiyya da na kananan hukumomi (11) dake shiyyar Funtua a dakin taro na H&B dake garin Funtua.
Hon. Yaro ya cigaba da bayyana irin taimakon da Hon. Hamza Sule Faskari ke yi ma al'ummar shiyyar Funtua wanda hakan ne ya basu dama na kirkirar wannan kungiya domin cigaba da fadi ma al'umma irin abubuwan da yake yi.
Sannan ya tabbatar ma da al'umma cewa" wannan kungiya bata siyasa ba ce ko wani neman takara, kungiya ce aka kafa domin cigaba da bayyana irin ayyukan alkairin da Hon. Hamza Sule keyi domin al'umma suyi ko yi.
Hon. Haruna Yaro ya mika godiyar sa ga gwamnan jihar Katsina Mal. Dikko Umar Radda bisa kyakkyawan shugabancin sa a jihar Katsina tare da rokon karin zaman lafiya da karuwar arziki a jihar Katsina.
Mutane da dama ne s**a gabatar da jawabai na fatan alkairi tare da tofa albarkacin bakin su akan ayyukan alkairi na Hon. Hamza Sule Faskari a wurin taron.
Bayan kammala jawabai a wurin taron an mika takardun k**a aiki ga shugabannin kungiyar matakin shiyya da kuma kananan hukumomin (11) da s**a fito daga shiyyar ta Funtua, taron ya samu halartar yan siyasa daga ko'ina a fadin shiyyar ta Funtua.