Atlas News Hausa

Atlas News Hausa I M Film Producer/Editor/actor In Kannywood

'Yan bindiga sun yi ajalin matafiya mutum 9 a jihar Filato, in ji wani rahoto da jaridar Daily Trust ta ruwaito.
14/09/2026

'Yan bindiga sun yi ajalin matafiya mutum 9 a jihar Filato, in ji wani rahoto da jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shin Naira 3,000 ta na isarku cin abinci cikin walwala na yini ɗaya a Nijeriya?Josef Onoh, tsohon dan majalisar dokokin ...
14/09/2026

Shin Naira 3,000 ta na isarku cin abinci cikin walwala na yini ɗaya a Nijeriya?

Josef Onoh, tsohon dan majalisar dokokin jihar Enugu, ya soki jakadan Nijeriya da aka nada zuwa Mexico, Reno Omokri, kan ikirarinsa cewa Naira 3,000 na iya wadatar da matsakaicin dan Nijeriya a rana.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Onoh ya ce maganar ta yi nesa da hakikanin rayuwar 'yan Nijeriya, musamman ganin hauhawar farashin abinci da sauran bukatun yau da kullum kamar sufuri, lafiya, ilimi da makamashi.

DCL Hausa

Da ɗumi-ɗumi: Shugaban Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu na Zaɓen 2027 Abdulaziz Yari Ya yi wa Sarkin Musulmi Sultan Of Sokoto Al...
14/09/2026

Da ɗumi-ɗumi: Shugaban Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu na Zaɓen 2027 Abdulaziz Yari Ya yi wa Sarkin Musulmi Sultan Of Sokoto Alƙawarin samawa Tinubu Kuri’u Milyan 20 a zaɓen na 2027.

Yari Ya bayyana Hakan a lokacin Ziyarar Fadar Sarkin Musulmin A Sokoto

Mata Musulmi 'yan Arewacin Nijeriya na goyon bayan tazarcen Tinubu
14/09/2026

Mata Musulmi 'yan Arewacin Nijeriya na goyon bayan tazarcen Tinubu

KANO VENDORS VIBES 10 IS COMING! Kana da sana’a? Kana da kaya da kake son tallatawa? Ko kana neman sabbin kwastomomi?Wan...
13/09/2026

KANO VENDORS VIBES 10 IS COMING!

Kana da sana’a? Kana da kaya da kake son tallatawa? Ko kana neman sabbin kwastomomi?

Wannan damar taka ce!

KANO VENDORS VIBES 10 – TRADE FAIR na zuwa da babbar dama ga ‘yan kasuwa da masu sana’o’i domin baje kolin sana’o’insu, tallata kayayyaki, samun sababbin kwastomomi da haɗuwa da sauran ‘yan kasuwa.

📅 1st & 2nd OCTOBER

💰 STALL FEE: ₦30,000

🍔 FOOD
🥤 DRINKS
🛍️ PRODUCTS
🎮 GAMES

Kada ka bari a baka labari. Ka yi rijista yanzu domin ka samu gurinka a wannan gagarumin taro.

📞 SPONSOR/ENQUIRIES:
07033023352

📧 [email protected]

👉 REGISTER NOW!





An Fara Gudanar Da Zagayen Mauludin Manzon Allah (S) Na Duka Gari a Katsina.Katsina Times.Al'ummar musulmi masoya Manzon...
13/09/2026

An Fara Gudanar Da Zagayen Mauludin Manzon Allah (S) Na Duka Gari a Katsina.

Katsina Times.

Al'ummar musulmi masoya Manzon Allah (S) na garin Katsina da kewaye, sun fito a ranar Lahadi 13 ga watan Satumba 2026, domin gudanar da zagayen mauludin Manzon Allah (S) na duka gari, kamar yadda aka saba gudanarwa a kowace shekara.

Tawagar babban limamin masallacin sarki, Sheikh Imam Mustapha ne a farko, yayin da sauran shehunan zawiyoyi, tawagar masu ishiriniya, masu karatun Alkur'ani mai girma, da al'umma daban-daban ke a bayan shi.

Zagayen wanda aka saba gudanarwa a kowace shekara, yana haɗa fuskokin al'ummar musulmi masoya Manzon Allah (S), da dama, a halin yanzu zagayen yana yana cigaba da tafiya cikin tsari kamar adda aka saba gudanarwa, ana hasashen cewa zagayen zai cigaba da kasancewa har zuwa yamma wannan rana.

📷Katsina Times

Zan mayar da mafi ƙarancin albashi Naira 500,000 kuma za a samu wutar lantarki mara yankewa idan na zama shugaban Nijeri...
13/09/2026

Zan mayar da mafi ƙarancin albashi Naira 500,000 kuma za a samu wutar lantarki mara yankewa idan na zama shugaban Nijeriya - Sowore

Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya yi alkawarin mayar da mafi ƙarancin albashi zuwa Naira 500,000 a duk wata ga ma’aikatan Nijeriya idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027.

Sowore ya kuma yi alkawarin samar da wutar lantarki ta tsawon sa’o’i 24 a kowacce rana, samar da ilimi kyauta da sauƙin samu a dukkanin matakai.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Sowore ya bayyana waɗannan tsare-tsare ne a wata hira da jaridar Independent, wadda aka wallafa ranar Lahadi, yayin da yake bayyana ajandar jam'iyyarsa ta AAC gabanin babban zaɓen 2027.

Hukumar REMASAB ta hana zuba yashi, yin aikin siminti ko ajiye kayan gini a kan tituna a fadin Jihar Kano.Ana kira ga ja...
13/09/2026

Hukumar REMASAB ta hana zuba yashi, yin aikin siminti ko ajiye kayan gini a kan tituna a fadin Jihar Kano.

Ana kira ga jama’a da su guji wannan dabi’a domin kare tituna da sauƙaƙa zirga-zirga.

Duk inda aka ga ana zuba yashi, siminti ko ajiye kayan gini a kan t**i, a kira lambobin wayar da ke ƙasa domin hukumar ta ɗauki matakin da ya dace.

0814 471 5099
0806 028 0898
0803 966 3977
0816 161 8400.

Farashin fetur ya tashi a sassan AbujaGidajen mai da dama a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya sun kara farashin lit...
13/09/2026

Farashin fetur ya tashi a sassan Abuja

Gidajen mai da dama a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya sun kara farashin litar man fetur daga N1,265 zuwa N1,350 kan kowace lita, wato karin N85.

Nawa ne farashin litar fetur a yankin da kuke a halin yanzu?

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron shugabannin BRICS karo na 18...
13/09/2026

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron shugabannin BRICS karo na 18, wanda ake gudanarwa a birnin New Delhi na ƙasar India. Shettima ya isa India ne domin wakiltar Najeriya a taron da ke haɗa manyan ƙasashe masu tasowa...

A yayin taron, Shettima ya gana da Firaministan India, Narendra Modi, yayin da shugabannin ƙasashe daban-daban s**a hallara a Bharat Mandapam, wurin da ake gudanar da taron...

Taron na bana ya mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki, kasuwanci, fasaha, makamashi, kiwon lafiya da ci gaba mai ɗorewa, tare da tattauna matsalolin da ke addabar duniya a halin yanzu...

Najeriya na ƙoƙarin amfani da kasancewarta cikin tsarin BRICS wajen ƙara samun damar zuba jari, kasuwanci, fasaha da haɗin gwiwar tattalin arziki da ƙasashe membobin kungiyar...

Firaministan India Narendra Modi ya kuma jaddada muhimmancin ƙarfafa haɗin kan ƙasashen Global South, tare da yin kira da a gyara tsarin hukumomin duniya domin ƙasashe masu tasowa su samu ƙarin tasiri wajen yanke shawarar da ta shafi duniya...

A ranar ƙarshe ta taron, Modi ya gana da shugabanni daga wasu ƙasashe, ciki har da wakilin Najeriya, yayin da taron ya ci gaba da tattauna batutuwan tattalin arziki, tsaro da siyasar duniya...

Muftahu Yahaya Mai Dandarani

Address

Kano
700001

Telephone

+2348036970125

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Atlas News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Atlas News Hausa:

Shortcuts

Share