30/07/2025
Babbar Kotun Jihar Katsina mai lamba 9, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a I.I. Mashi, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutum biyu – Shamsu Lawal, tsohon mai gadi, da Tasi’u Rabi’u, mai girki – bayan ta tabbatar da cewa su ne s**a kashe tsohon Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na Jihar Katsina, Hon. Rabe Nasir, a shekarar 2021.
Wannan hukunci ya zo ne bayan shekara huɗu da faruwar lamarin da ya tayar da hankali a fadin jihar da ma ƙasar baki ɗaya.
Tarihin Marigayin:
Hon. Rabe Nasir ya kasance ɗaya daga cikin manyan 'yan siyasa da s**a taka rawa a jihar Katsina. Ya taba rike mukamin Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, sannan ya yi aiki a hukumar tsaro ta DSS kafin daga bisani ya shiga siyasa.
Yadda Aka Kashe Shi:
Binciken asibiti da na rundunar ‘yan sanda ya tabbatar da cewa mutanen biyu – wadanda s**a kasance ma’aikatan gidan marigayin – sun haɗa guba da abinci s**a ba shi, wanda hakan ya raunata shi matuƙa. Daga bisani, s**a caccaka masa wuka har lahira.
Lamarin ya faru ne a gidansa da ke unguwar Fatima Shema a birnin Katsina a ranar 3 ga Disamba, 2021. Bayan kisan, ‘yan sanda sun k**a wadanda ake zargi, kuma daga bisani s**a gurfana a gaban kotu inda aka gabatar da hujjoji da shaidu masu ƙarfi da s**a tabbatar da laifin nasu.
Hukuncin Kotu:
Bayan dogon shari’a da shaidu na kwarara, kotu ta tabbatar da laifin kisan kai, ta kuma yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Masu fashin baki na ganin cewa wannan hukunci zai zama izina ga wasu da ke da niyyar aikata laifi mak**ancin haka a nan gaba, kuma hakan na daga cikin ƙoƙarin tabbatar da doka da oda a cikin al’umma.
|Katsina Times.