
02/09/2025
Maigirma Dan Majalissar Dokoki ta Jahar Katsina mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa Hon Tukur Iliyasu Shagumba na Mika Sakon taya Murna zuwa ga Hon Tasi'u Dahiru Dandagoro PhD Tshohon Kwamishinan Ayyukan Gidaje da Sufuri na Jahar kuma Sabon S'A Wanda Maigirma Gwamnan Jahar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya bashi
Maigirma Gwamnan Jahar Katsina Malam Dikko Umar Radda PhD ya nada Hon Tasi'u Dahiru Dandagoro PhD akan Mai bashi Shawara akan Ilimin Addini da kuma Tallafama Yaran da s**a Kasa Cigaba da Karatun Boko Dana Addini domin ganin anjawosu jiki an sai ta masu rayuwarsu domin su zama Jakadu na gari a cikin Al'ummah
Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissa mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa ya godema Maigirma Gwamnan Jahar Katsina Malam Dikko Umar Radda PhD da wannan Mukamin da Yaba Hon Tasi'u Dahiru Dandagoro da Sauran Mukaman da Yaba Al'ummar Karamar Hukumar Batagarawa
DAGA
HON Muzambil Gide Batagarawa S'S'A Media to Hon Tukur Iliyasu Shagumba Dan Majalissa mai Wakiltar Karamar Hukumar Batagarawa
Date 02/09/2025.