Gwagware MEDIA Reporters

Gwagware MEDIA Reporters News update about His Excellency Malam Dikko Umaru Radda activities in Government and Politics

31/08/2026

Kai tsaye daga ofishin Shugaban hukumar ilimin matakin farko dana sakandare na Jihar katsina Hon. Yusuf Suleman Jibia

31/08/2026

Kai tsaye daga ofishin Kwamishonan Ma’aikatar Bunkasa jin dadi da cigaban yankunan karkara Prof. Abdulhamid Ahmed

29/08/2026

Daga birnin tarayya ayau
29/08/2026

Dr. Dikko Umaru Radda LIVE GreatestHighlights The Following Gwagware MEDIA Reporters Katsina Post Mobile Media Crew Jbc Viral fans

Gwamna Raɗɗa Ya Gana da Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima a AbujaGwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya gana...
29/08/2026

Gwamna Raɗɗa Ya Gana da Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima a Abuja

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya gana da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, a gidansa da ke Abuja.

Ganawar, wadda ta gudana a daren ranar Laraba, ta kuma samu halartar Dr. Mustapha Muhammad Inuwa, wanda ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a baya-bayan nan.

Kodayake ba a bayyana cikakkun bayanai kan abin da aka tattauna ba, ana kyautata zaton cewa ganawar ta mayar da hankali kan wasu muhimman batutuwan siyasa da s**a shafi Jihar Katsina da kuma sauran al’amuran siyasar ƙasa.

Daga cikin waɗanda s**a raka Gwamna Raɗɗa akwai Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir; fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Dahiru Barau Mangal; da tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, Arc. Ahmed Musa Dangiwa.

Sauran waɗanda s**a halarci ganawar sun haɗa da ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Musawa/Matazu, Hon. Abdullahi Aliyu Dujiman Katsina; ɗan takarar jam’iyyar APC mai neman wakiltar Katsina a Majalisar Wakilai ta Tarayya, Hon. Barr. Abba Mangal; da kuma Hon. Shamsu Sule Funtua na jam’iyyar APC a Jihar Katsina.

KATSINA BA FILIN RABA IKON SIYASA BA CE — GWAMNA RADDA SHINE JAGORAN APC A JIHAR KATSINAA siyasar Katsina, ya kamata kow...
24/08/2026

KATSINA BA FILIN RABA IKON SIYASA BA CE — GWAMNA RADDA SHINE JAGORAN APC A JIHAR KATSINA

A siyasar Katsina, ya kamata kowa ya fahimci abu ɗaya: Malam Dikko Umar Radda, PhD, CON, shi ne zababben Gwamnan Jihar Katsina kuma jagoran siyasar APC a jihar. Don haka duk wani babban ɗan siyasa da zai zo Katsina, komai matsayinsa, ya kamata ya mutunta tsarin siyasa da jagorancin da mutanen Katsina s**a amince da shi.

Ba muna cewa wani ba shi da damar yin siyasa ba ne; kowa yana da ’yancin siyasa. Amma ba za a gina siyasa mai ɗorewa ta hanyar tsallake jagorancin Gwamna ko ƙoƙarin ƙirƙirar wani cibiyar iko a bayan fage ba. Idan ana son haɗin kan APC a Katsina, hanya mafi dacewa ita ce a mutunta Gwamna Radda a matsayinsa na jagoran siyasar jihar.

Gwamna ya yi haƙuri, ya yi shiru, ya girmama kowa. Amma wannan ba yana nufin ku ɗauki haƙurinsa a matsayin izinin raina matsayinsa ba. Siyasa tana da dokokinta: wanda aka ɗora wa jagoranci a jihar, a mutunta shi; wanda yake son fafatawa, ya fito fili. Katsina ba ta buƙatar shugabannin bayan fage—Katsina tana da jagora, kuma sunansa Dikko Umar Radda.

22/08/2026
22/08/2026

Celebrating my 5th year on Facebook. Thank you for your continuing support. I could never have made it without you. 🙏🤗🎉

Gwamnatin Katsina Ta Tabbatar Da inganga jindadin Ma’aikata Bayan RitayaGwamnatin Jihar Katsina ta ce a shirye take ta s...
19/08/2026

Gwamnatin Katsina Ta Tabbatar Da inganga jindadin Ma’aikata Bayan Ritaya

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce a shirye take ta samar da kyakkyawan yanayin rayuwa ga ma’aikata a lokacin da suke aiki da kuma bayan ritayarsu.

Mai ba Gwamnan shawara kan Gyaran Harkokin Aikin Gwamnati, Alhaji Usman Isiyaku, ya bayyana hakan yayin wani taron wayar da kai kan Sabuwar Dokar Fansho ta 2025.

Ya ce gwamnatin na son tabbatar da cewa ma’aikacin da ya yi shekaru yana yi wa gwamnati aiki cikin gaskiya, ya samu ritaya cikin mutunci tare da cikakken hakkinsa.

A sabon tsarin, ma’aikaci zai bayar da kashi 7%, yayin da gwamnati za ta bayar da kashi 13% na albashinsa.

Katsina na daga cikin jihohi tara cikin 36 da s**a rungumi sabon tsarin domin inganta harkokin fansho da walwalar masu ritaya.

General Notice
19/08/2026

General Notice

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gwagware MEDIA Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Gwagware MEDIA Reporters:

Shortcuts

Share