
27/09/2022
Zawiyyar Alheri Ta Gwangwaje Kungiyoyin Kwallon Kafa Na Shiyyar Funtua Da Rigunan Yan Wasa Da Kwallo
Zawiyyar Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dr Mustapha Muhammad Inuwa, ta samar da tallafin Rigunan Sanyawa na Yan Wasa da kuma kwallo ga Kungiyoyin 24 da s**a fito daga Shiyyar Funtua.
Shugaban Zawiyyar Dr.Mustapha Muhammad Inuwa ne ya gabatar da tallafin ga Kungiyoyin da s**a amfana a yayin wani taro da ya gudana a Ofishin Yakin Neman Zaben shi da ke Cikin Birnin Katsina.
Tsohon Sakataren Gwamnatin wanda kuma tsohon mai neman takarar Gwamnan Jihar Katsina ne, ya bukaci Matasa akan su rungumi harkokin Wasanni domin dogaro da kan su, maimakon jiran aikin gwamnati.
A cewar shi, Zawiyyar ta yi kudirin shirya gasar kwallon kafa ne ga Kungiyoyin, to sai dai a sabili da yanayin Matsalar tsaro da Shiyyar ta Funtua ke fama da shi Hakan bai yiwu ba.
A sabili da Haka ne aka yanke shawarar samar da tallafin kayayyakin wasan ga Kungiyoyin kamar yadda aka alkawarta.
Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa ya yi amfani da damar wurin sanar da mabiyan shi a harkokin siyasa cewar, su shirya tsaf domin bude wani Sabon babi da zai yi a siyasar shi.
A nashi jawabin, Khalifan Zawiyyar Alhaji Hamisu Hara, ya bayyana cewa Zawiyyar ta Shirya gasar kwallon kafa a shiyyoyin Katsina da Daura, sai dai na Shiyyar Funtua bai samu yiyuwa ba a sabili da yanayin tsaro a Shiyyar.
Ya tabbatar da cewar, zasu cigaba da kasancewa a tare da Dr.Mustapha Inuwa, a duk inda ya nufa a harkokin siyasar shi.
Alhaji Hamisu Hara ya sanar da cewa Zawiyyar ta kashe miliyoyin kudi domin shirya gasar, Wadda ke da nufin tallafawa matasa, tare da kara masu kwarin guiwa akan su rungumi harkar Wasanni domin dogaro da kan su.
Sauran wadanda s**a maganta a lokacin taron sun hada da Shugaban Kwamitin Harkokin Wasanni na Zawiyyar Alheri Aminu Musa, sai wasu daga cikin wakilan Kungiyoyin da s**a amfana.