11/02/2023
Me Ya Sa Hukumar Kidaya Ba Ta Tantance Wadanda S**a Nemi Aikin Kidaya Na Yankin Wakilin Arewa 'B' A Karamar Hukumar Katsina Ba?
Daga Mohammad A. Isa
Korafe-korafe sun yawaita daga al'ummar da s**a fito daga yankin Wakilin Arewa 'B' a karamar hukumar Katsina, kan yadda hukumar kidaya ta jiha ta tsallake tantance mutanen yankin wadanda s**a nemi aikin wucin gadi wanda hukumar za ta gudanar a shekarar nan ta 2023, alhali a cewarsu sun cike duk sharuddan da ake nema na tantancewar, har ma an saki sunayensu tare da lika sunayen nasu su kimanin 285 a ofishin Hedikwatar hukumar Kidayar ta Jiha domin tantancewa.
Al'ummar sun bayyana mani cewa, hukumar ta saki jadawalin ranakun tantance kowane rukunin al'umma na yankunan karamar hukumar ta Katsina (Wards) a ofishin hikimar, inda a jadawalin, hukumar ta sanya ranar Lahadi 5 ga watan Fabrairun 2023 a matsayin ranar da za ta tantance mutanen da s**a fito daga yankin na Wakilin Arewa 'B', sai dai da mutanen yankin s**a halarci Hedikwatar tancewar a ranar da aka ayyana masu, tun da sanyi Safiya har zuwa Yammaci ba su ga keyar ko mutum daya daga cikin ma'aikatan tantancewar ba tsawon yin, daga bisani ne ma s**a sami sakon cewa ma'aikatan sun ce ranar ba za su yi aikin tantancewar ba, sai dai su dawo kashegari (Litinin 6 ga Fabrairu).
Al'ummar sun ci gaba da bayyana mani cewa, kashegari da s**a sake dawowa k**ar yadda aka umurce su, shi ma tun da sanyin safiya har rana ta yake ba su ga keyar kowa ba, sai ma wani sako marar dadi da s**a samu daga ma'aikatan cewa a fadawa mutane cewa su fa sun riga da sun rufe tantancewar tun a ranar Lahadi, don haka kowa ya k**a gabansa.
Bayan gama jin korafe-korafen al'ummar yankin, na garzaya zuwa ofishin shugaban riko na yanki da al'ummar Wakilin Arewa 'B' din s**a fito wato Galadiman Arewa. A tattaunawar da na yi da Galadiman Arewan, ya bayyana mani cewa; duk da yake su ne Sarakunan jama'a, amma hukumar kidayar ba ta saka su a cikin sha'anin aikin ba, b***e su san abin da yake zuwa yana dawowa a cikinsa. Don haka kawai kowa ya hakura da aikin tun da an ce an rufe.
Haka kuma, na yi tattaki zuwa Hedikwatar hukumar don jin ta bakinsu a kan korafe-korafen da jama'ar ke yi a kansu dangane da rashin tantance su, amma dai magana daya tilo ce amsar, "an rufe tantancewar tun ranar Lahadi."
Wasu mutane sun tsegunta mani cewa, duk da an ce an rufe tantancewar, amma suna lura da wasu mutane na gittayya a hukumar, suna kai Sunayen da Lambobin rajistarsu na aikin Kidayar, wanda suke zargin kila masu uwa a bakin murhu ne za a tantance su ta bayan gida.
"Meye matsayinmu a yanzu da ba a tantance mu ba? A matsayinmu na 'yan k'asa da muka cika sharuddan zama 'yan kasa kuma muka cika sharuddan yin aikin a matakin farko (domin har sunayensu ya fito saura tantancewar), shin yanzu an soke mu ne a cikin tsarin aikin, ko kuwa? Idan an soke mu ne, meye dalilin sokewar, kuma me ya sa ba a yi mana bayani don mu san matsayinmu ba?" Tambayoyin da al'ummar na Arewa 'B' ke yi kenan.
Yankin Wakilin Arewa 'B' dai yanki ne da ke cikin birnin katsina tsamo-tsamo, wanda yake da dubban al'ummma da s**a hada da 'yan Boko, Ma'aikatan gwamnati, 'yan Kasuwa, Dalibai, da wadanda s**a kammala Karatu a Manyan makarantu da sauransu.