12/06/2025
SHAWARA!!!
Duk wani ɗan siyasa da ya ba ku Taliya ko kuɗi da sauran su ku karɓe kuma ku zaɓi cancanta. Da shi ne suke ganin za su yaudare mu mu ƙara zaɓar su a zaɓe mai zuwa.
Ya kamata mu waye. Domin mu ne ke shanye dukkan baƙar wahalar da take faruwa a sanadiyyar rashin iya mulkin su, da son zuciyar su, da zaluncin su.
Wallahi duk wanda bai kamanta dai-dai ba mu yi duk yanda za mu yi don ganin mun canza shi da wanda muke tsammanin zai kamanta mana.
Makauniyar soyayya da son zuciya ke wahalar da mu a rayuwar mu.