04/11/2025
Sanata Abdulaziz Yar’adua Ya Tallafama Matasa Masu Ƙananan Sana'oi Da Jari A Mazabar Katsina Ta Tsakiya
Bisa kokarin Sanata Abdu Soja Sanata dake wakiltar shiyar Katsina ta tsakiya a majalissar dattawan najeriya ta goma na tallafama al'ummar mazabar sa musamman masu kananan jari, Ranar Litinin ya kaddamar da bayar da tallafin kudi ga masu ƙananan kasuwanci bayan basu kyautar POS Machine don s**ara habaka kasuwancin nasu, Inda mutane dari biyu da sittin 260 s**a amfana da tallafin dubu ashirin da biyar biyar, shirin wanda zai game masu kananan kasuwancin har su dari hudu 400.
Uwargida Dr Mrs. Esohe Grace Ilori wadda itace ke saka ido kan shirin ta jinjina ma Sanatan bisa wannan hangen nesa dayayi na tallafama masu kananan kasuwanci inda tayi kira ga waɗanda s**a amfana da shirin da su tabbatar sunyi amfani dashi ta hanyar da ya dace.
Shima Sanatan wanda yasamu wakilcin Alhaji Tanimu Garba ya ja hankalin waɗanda s**a amfana da shirin da su yi amfani da abinda s**a amfana dashi ta hanyar da yadace kuma tabbatar masu da cewar yanzu haka ana aikin samar masu da takardar rijistar shaidar kasuwancin ta kasa wato Co-operate Affairs Commission Certificate wanda da zaran an kammala zasu kira kowa abashi Insha Allah.
Daga cikin waɗanda s**a tofa albarkacin bakinsu a wajen taron akwai Ambassador Yakubu Sulaiman, Shugaban Jam'iyar APC na shiyar Katsina wanda yasamu wakilcin Shugaban Jam'iyar APC na Ƙaramar Hukumar Katsina, Mai kula da shirin Malam Abdullahi Hassan da dai sauran su.
Suma waɗanda s**a amfana da shirin sun bayyana jindadin su da godiyar su ga Sanatan, sunkuma tabbatar zasuyi amfani da tallafin ta hanya mai kyau.
Shirin wanda zai cigaba nan bada jimawa ba inda za'a kammala ma sauran mutane dari da arba'in 140.
Sen. Abdu Soja Media Team.