Muryar Funtua

Muryar Funtua Labarai da dumi-duminsu

18/07/2026

Duk wanda zai shiga Birnin Makka Dole Ne sai Ya shigo ta wannan Mashigar.

Kuyi masa salati sannan kuyi mana shearinng domin ku qara qarfafa mana gwuiwa.

MAF Multimedia

Gamu kusa da qabarin sayyada nana khadija Rd)
27/02/2026

Gamu kusa da qabarin sayyada nana khadija Rd)

Wannan Itace Rijiyar Babban Sahabin Manzon Allah (Saw) Abu Dhalha (Rd) Wadda Manzon Allah yakasance  Yana shan Ruwan Cik...
01/01/2026

Wannan Itace Rijiyar Babban Sahabin Manzon Allah (Saw) Abu Dhalha (Rd) Wadda Manzon Allah yakasance Yana shan Ruwan Cikin ta.

Wannan Alamar dakuke kallo Tana cikin Masallacin Manzon Allah (Saw) ne Kuma Itace ainufin Rijiyar da Abu Dhalha Ya mallaka wadda Ake amfana da Ruwan Cikin Ta.

Abu Dhalha yakasance daya daga cikin Sababbai mafiya tarin Dukiya Mai gonakin dabino da apple da gonakin jiminu da dai sauransu.

Hakika wannan Wurin yakasance Wurin tunawa dashi tsawon Sama da shekara 1400.

Sannan wannan Rijiyar tana daya daga cikin rijiyoyi Har bakwai wadanda Manzon Allah (Saw) yakasance Yana shan Ruwan Cikin su.

Duk Wanda Baizoba Allah Yakawoshi Wanda kuma yazo Allah yasa yanada rabon dawowa Amen 🙏

Kuyi masa salati sannan kuyi Mana shearingg Domin ku kara qarfafa Mana Gwuiwa 🙏

MAF Multimedia 📹 Maf Multimedia Fans 📹

Wannan Shine qabarin Sayyada HALIMATU SA'ADIYA (Rd) Halimatus Sa'adiya ita ce ta shayar da Manzon Allah (Saw) tsawon she...
31/12/2025

Wannan Shine qabarin Sayyada HALIMATU SA'ADIYA (Rd)

Halimatus Sa'adiya ita ce ta shayar da Manzon Allah (Saw) tsawon shekara biyu, a bisa al'adar larabawan Makka ida s**a haifi abin haihuwa , sai su mika shi izuwa larabawan Kauye domin ya kware da fasaha irin ta mutanan kauye. Kamar yadda ya zo a cikin hadisi.

An ruwaito ga Halimatu Sa'adiyya cewa,

"na zo Makka a cikin mataye daga bani Sa'adin dan Bakarin domin neman shayarwa da jaririnmu da awakanmu wadanda wallahi ba sa bubbugo da nono daga hatsansu ko da dugo daya".

" Kuma muna kwana har gari ya waye jinjirinmu bai samu nono da zai tsotsa a kirjina ba, wanda zai kosar da shi kuma bai samu nonon da zai kosar da shi a hantsar dabbobinmu ba (Sabo da tsananin fari) har dai muka iso Makka.

Na rantse da Allah ban san wata mata ba (daga cikinmu ) sai da aka zo mata da manzon Allah (SAW) sai ta ki daukansa saboda an ce shi maraya ne ta bangaran mahaifinsa. Kuma wallahi babu wata mata daga cikin kawayena face sai da ta daukko abin shayarwa wanisa."

"Ni kuma a yayin dana rasa wani abin shayarwa waninsa, sai na ce da mai gidana, ni ina jin kunyar na koma a cikin kawayena ba tare da na samu abin shayarwa ba, zan je izuwa wannan maraya wallahi na dauko shi.

Sai na tafi dakko shi, sai kuwa na same shi a nannade a cikin tufafi, na ganshi mafi tsananin haske akwai shimfidar koriya yana yin barci akan shimfidarsa akan keyersa.

Yana mai runtse idanuwansa, sai na ji tausayinsa kada na tashe shi daga cikin barcinsa saboda kyawunsa da cikar suffarsa.

Sai na matso kusa da shi sannu-sannu, sai na dora hannuna akan kirjinsa, sai ya yi murmushi irin na dariya, sai ya bude idanuwansa yana duba izuwa gare ni. Sai wani haske ya fito daga idanuwansa har dai ya shiga tsakanin idanuwana,
Kuma sai na ba shi nono na dama, sai ya karba ya sha gwargwdon yadda ya so na daga nono, sai kuma na juya shi izuwa na hagun sai ya ki karbarsa, haka dai halinsa ya kasance ya sha na dama ya barwa dan uwansa na hagun. (Saw)

Kadan Kenan Daga Cikin labarin wannan baiwar Allah.

Duk Wanda Baizoba Allah Yakawoshi Wanda kuma yazo Allah yasa yanada rabon dawowa Amen 🙏

Kuyi Masa salati sannan kuyi Mana shearingg Domin ku kara qarfafa Mana Gwuiwa 🙏

MAF Multimedia 📹 Maf Multimedia Fans 📹 Muhammad Aliyu Kannywood Aminu Ladan Abubakar

Wannan Shine wani Bangaren cikin birnin Madinar Annab! Muhammad (SAW)Shin Me kuka sani Dangane da Tarihin SA (Sallallahu...
30/12/2025

Wannan Shine wani Bangaren cikin birnin Madinar Annab! Muhammad (SAW)

Shin Me kuka sani Dangane da Tarihin SA (Sallallahu alaihi wasallam)

Tarihin Annabi Muhammadu (SAW) A Taƙaice Cikin Farin Ciki da Jin Daɗi Da Nishadi.

1. Haihuwarsa da Asalinsa

Annabi Muhammadu (SAW) an haife shi ne a garin Makka a shekara ta 570 Miladiyya, wato shekara da ake kira Shekarar Giwaye, shekarar da Abraha ya kawo rundunar giwaye don rus@ Ka'aba, amma Allah ya hal@ka su da tsuntsaye masu jifa da duwatsu.

Sunansa Muhammadu ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muṭṭalib, daga zuriyar Annab! Isma’il ɗan Annabi Ibrahim (AS). Mahaifinsa ya r@su tun kafin a haife shi, mahaifiyarsa kuma, Amina, ta r@su yana ƙarami.

2. Ƙuruciya da Halayensa

Yayin da yake ƙarami, ya girma ne a wajen wata mace mai suna Halima Sa’adiyya, wadda ta raineshi a karkara. Wannan ya taimaka wajen koshin lafiyarsa da lafazzinsa mai tsabta.

Ya kasance mai gaskiya, amintacce, har ma mutanen Makka suna kiransa da "Al-Amin" (Amince).

3. Auren Sayy!da Khadija

Yana da shekara 25, ya yi aure da Sayyida Khadija bint Khuwayl!d, wata babbar mace mai arz!ki kuma mai daraja. Ita ce mace ta farko da ta karɓi Musulunci kuma ta kasance garkuwa gare shi.

4. Farkon Wahayi

Yana da shekara 40, yana yin tunani a Dutsen Hira, sai Mala’ika Jibrilu ya zo da saƙo daga Allah:

"Karanta!" (Ikra’)
Wannan shine farkon saƙon Annabci wanda ya kai shekaru 23 yana yada shi.

5. Gwaji da Ƙoƙarin Yada Saƙo

A Makka, mutane da yawa sun ƙi karɓar saƙonsa, musamman ‘yan mulkin Qur@yshawa. Sun tsananta masa da sahabbansa, sun ƙuntata musu, har aka tilasta wasu yin hijira zuwa Habasha.

6. Hijira zuwa Madina

Daga ƙarshe, Allah ya buɗe masa ƙofa ta neman mafaka a garin Madina. Ya bar Makka tare da abokinsa Abu Bakr As-Siddiq (RA). Wannan hijira ce ta haifar da sabuwar rayuwa ga Musulmi.

7. Madina da Jihad!

A Madina ne Annabi (SAW) ya kafa al'umma ta Musulunci bisa adalci, gaskiya, da zumunta tsakanin mabiya. An yi wasu yaqe-yaƙe don kare Musulunci kamar Badr, Uhud, da Khandaq.
Koda kuwa an yi yaƙ!, Annabi bai taɓa zaluntar kowa ba, har da maƙiyansa ya dinga gafarta musu.

8. Ƙarɓar Makka

Bayan shekara 8 da hijira, Annabi (SAW) ya koma Makka cikin nasara da ladabi. Bai rama azabar da aka masa ba, ya ce:

"Ku tafi, kun ‘yanta, babu laifi a kanku."
Wannan ya nuna ƙasaitar zuciyarsa da rahamar zuciyarsa.

9. Rasuwa

A shekara ta 11 bayan hijira (632 Miladiyya), Annabi (SAW) ya r@su yana da shekara 63. Ya rasu a cikin dakin matarsa mai ƙauna A’isha (RA), kuma aka binne shi a can.

Daga Qarshe.

Annabi Muhammadu (SAW) rahama ne ga duniya baki ɗaya. Ya zo da saƙo na gaskiya, adalci, da soyayya. Ya nuna mana yadda za mu zama mutane na gari, miji nagari, shugaba adali, da makwabci mai ƙauna.

Allah kasanya mu acikin cetonsa (Saw) Duk Wanda Baizoba Allah yasa yanada rabon zuwa Wanda kuma yazo Allah yasa yanada rabon dawowa Amen 🙏

Kuyi Masa salati sannan kuyi Mana shearingg Domin ku kara qarfafa Mana Gwuiwa 🙏

MAF Multimedia 📹 Maf Multimedia Fans 📹 Muhammad Aliyu Kannywood Aminu Ladan Abubakar

Address

Zaria Road Funtua
Katsina
820101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Funtua posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share