17/09/2025
Idan har Tinubu bai gyara ba, a 2027 ba zan zabe shi ba, sai dai a kore ni a APC - Kalou Dan Batsari ya ɗau zafi
Daga Kalou ɗan Batsari.
Jama’a ku zama shaida na rantsi da girman Allah idan shugaban ƙasa bai gyara wasu kura-kurai ba, to bazan zaɓe shi a zaɓen 2027 ba sai dai a koreni daga APC ko kuma inyi shinkafa da taliya!
Jama’a inason ku gane cewa lokaci ya yi daya kamata mu riƙa tsayawa muna lissafa irin yadda yan siyasar da muka zaɓa suke jagorantarmu bayan mun zaɓesu, domin hakan ya zama wani ma’auni da zamu yanke masu hukunci a zaɓen gaba.
Domin Allah na tsaya na lissafa na kuma gano cewa duk wani shugaba ko wakilin da na zaɓa, amman ya gaza akan abubuwa kaso 70 a cikin 100 na abinda nike tsammani daga gareshi ya yi, to wallahi bazan sake zaɓen shi ba!
Ko’a cikimmu akwai kujerun da bazan sake zaɓen su ba koda ace sunci zaɓen cikin gida wato na fidda gwani kenan, saboda irin yadda s**a kasa tare da gazawa wajan kyautata ma Al, ummar da s**a sha wahala s**a zaɓe su, shi yasa mukeson a bari ayi zaɓen fitar da gwani tunda siyasar dimukuraɗiyya ce muke yi ba ɗoki ɗora ba.
A yanzu tsawan shekara biyu kenan cif, akwai abubuwa da yawa da zan iya lissafowa wanda gwamnatin tarayya ta ƙirƙiro wanda kai tsaye a wurina domin Allah ya cutar dani a matsayina na ɗan ƙasa! wanda kuma in aka kwatanta da wanda kuma tayi ya taimaki rayuwata to baikai wanda na sha wahala ba. Misali:
1. Cire tallafin mai
2. Cire tallafin wuta
3. Tsadar data
4. Saka haraji a bankuna da sauransu barkatai.
Haka zalika akwai abubuwan da ake ɗaukewa daga arewa a mayar dasu kudu wanda babu wani dalili mai ƙarfi nayin hakan da ya gamsar dani . Ina son musani cewa lokacin yin wata siyasa ta gaba ɗaya saboda aƙidar party koda mutum baiyi abinda ya kamata ba, to domin Allah ya wuce.
Abinda nike tsammani shine duk garin da aka samu attack na yan bindiga da yayi sanadiyyar kashe aƙalla mutum 5! to ya kamata ace shugaban ƙasa ya zo wannan garin domin jajanta ma Al,ummar wannan yankin ko kuma ya naɗo kwamiti daga fadar shi domin jajantama al,ummar wannan yankin tunda suma sun zaɓe shi, kai koda ma basu zaɓe shi ba tunda suma yan ƙasa ne, inkau har bai iya zuwa to suma sai inga bai kamata su zaɓe shi ba.
Tabbas kamar yadda nasha faɗa a baya mai girma gwamnan jihar katsina malam Dikko umar Raɗɗa ya zuwa yanzu ya cimma abubuwa da yawa a nan jihar waɗanda sun taimaki Al,ummar jihar katsina ƙwarai da gaske, to amman gaskiyar magana muna muƙatar buƙatar kulawa ta musamman daga gwamnatin tarayya akan abubuwa da yawa a katsina da ma arewa baki ɗaya bawai iya katsina kaɗai ba, duba da irin wahalar da mutanammu suke sha! Ko yanzu a cikin damanar nan kazo ƙaramar Hukumata ta Batsari kaga irin yadda magidanta ke kwana waje dasu da iyalansu sakamakon rushewar gidajen su da ruwa yayi kuma basu da kuɗin gyara shi, amman sai zaɓe ya zo kuma ace kowa ya ɗauko katin zaɓen shi! 😭
Amman ayi mugani in tusa na hura wuta.