
27/08/2022
Al'ummar yankin Binoni suna cikin wani hali na rashin kyakykyawar Hanya!!!...
Inji wani Dan kishin kasa Comrd Adam Hashim Binoni
Duba da irin zunzurutun kudi da al'ummar garin Binoni muka sakawa Kungiyar IFAD CASP a karkashin jagorancin CDA/FSA na garin domin samun kashi tara(9) nayin wannan hanyar, cikin ikon Allah hakar mu ta cimma ruwa inda muka gina Kwalbatai biyu na shiga garin Binoni a kan kudi Naira Miliyan Ukku daidai.
Bisa Jarabawa ta ubangiji, a daminar farko tayin wannan aikin ruwa ya zaizayi kwalbati daya, daya kuwa ya janyeta baki daya.
Hakika mutanen Binoni, mutane ne masu kokari wajen yin aikin gayya da hadin kai domin ganin garin yaci gaba da alummar yakin baki daya, dukda duba da cewa a wannan aikin abin ya rigaya yapi karfin mu, sak**akon Hausawa kance "Hannu baya daukar Jikka shi kadai"!.
Munyi karaye-kiraye a gwabnati a wannan lokacin domin ta saka hannu ganin cewa an tallafa mana tun kafin haka ta afku, amma ba amo ba kida ko wani labari mai dadi akan aikin wannan hanyar.
Zaman da ake yanzu haka ko babur baya shiga garin saida 'yan dubaru, uwa uba Motar ita bama a maganarta.
Da wannan ne muke kara kira ga gwabnati ta taimaka ta duba koken domin ceto rayuwar mu dama sauran al'ummar yankin baki daya. 🙏
Rubutawa ; Adam Hashim Binoni.