
05/07/2022
'YAN NAJERIYA 10 DA SUKAFI KOWA WAUTA:
1. Dalibin da yake zaune a gida saboda yajin aiki, amma ba ya da katin zaben da zai canja shugabannin da s**a jefa shi cikin wannan hali.
2. Dalibin da ya gama karatu, yana zaune gida shekara da shekaru babu aikin yi, kuma ya kasa mallakar katin zabe.
3. Talakan da ke kuka da tsadar rayuwa, kuma ya kasa zuwa ya mallaki katin zabe.
4. Ma'aikacin da ya yi shekara da shekaru babu karin albashi, kuma ya kasa mallakar katin zabe.
5. Dan kasuwar da kasuwancinsa ya tabarbare sak**akon hauhawar farashi da rashin ciniki, ya kuma kasa mallakar katin zaben.
6. Manomin da 'yan bindiga s**a hana noma, kuma ya kasa mallakar katin zaben da zai canja shugabannin da s**a kasa ba shi tsaro.
7. Mutumin karkara da 'yan bindiga s**a hana zama gida, kuma ba ya da katin zabe.
8. Mutumin birni da yake fama da matsalar ruwa da wuta, amma ba ya da katin zabe.
9. Macen da ta rasa mijinta ko danginta saboda rashin tsaro, amma ta kasa mallakar katin zabe.
10. Wawan wawaye shi ne wanda ya mallaki katin zabe amma ya ki fita ya yi zabe, wai ko ya jefa kuri'a ba ta da amfani.
Jama'a mu yi kokari mu mallaki katin zabe. Katin zaben nan shi ne makamin talaka da zai yaki shugabanni 'yan jari-hujja. Yanzu haka hukumar zabe ta tsawaita lokacin karbar kati har zuwa wani lokaci.
Allah ya zaba mana shugabanni na gari.
In kunne yaji jiki yayi Arziki.