
13/09/2025
GAGGARUMIN FARETIN GIRMAMAWA GA MANZON ALLAH (S A W) A DA'IRAR KATSINA
kamar kowacce shekara ƴan'uwa Almajiran Shaikh Zakzaky (H) na Da'irar Katsina, ƙarƙashin Lajnar Islamiyyu na shirya gaggarumin Faretin Girmamawa ga Manzon Allah (s a w), Wanda ƴan Islamiyyu ke gabatarwa.
A wannan shekarar ma a yau Asabar 13/9/2025 - 20/3/1447 an shirya wannan Faretin domin Girmamawa tare da Faranta ran Manzon Allah (s a w). A kan shirya Faretin ne tsakanin Islamiyyun dake Da'irar Katsina baki ɗaya.
Akwan Group (A&B), masu taka Faretin, wanda akan fara kiran (Group B) ne, bayan sun kammala sai (Group A), sannan a lokaci guda kuma ga Alƙalai masu kula da ƙa'idojin Faretin suna lura domin fidda Zakarun da s**a fi nuna bajintarsu.
Daga cikin Islamiyyun da suke halarta a cikin (Group B) akwai: Ɗariƙil Huda Masanawa, Shabbabul Mahdi (a t f), Dinil Islam, Ansarul Mahdi (a t f), da sauransu. Sannan daga cikin (Group A) akwai: Tahriƙil Islam, Irshadussubyan, Fudiyayya Jibia, Fudiyyah Batagarawa, Tarbiyyatul Islam, da sauransu.
Bayan kammala wannan gaggarumin Faretin sai taƙaitaccen jawabi daga wasu ba'adin mutanen da aka gayyato tare da basu shaidar girmamawa (Certificate), daga nan kuma sai Malam Shehu Ɗalhatu Ƙarƙarku ya gabatar da jawabin rufewa.
Malam yayi taƙaitaccen jawabi akan shi manufar shirya irin wannan taron domin kusanto da sauran Al'ummar da muke rayuwa cikinsu, kamar yadda su Malam Zakzaky (H) suke irshadi akai, har yana cewa: “Su Malam Zakzaky (H) s**an ce idan za'a shirya irin wannan to a gayyato sauran ɓangarorin mutane da muke rayuwa tare dasu domin su fahimce mu, kuma ba muna cewa ka ajiye fahimtar ka ba kazo kayi tamu ba, a'a ka fahimce mu, mu fahimce ka, amma mu haɗu a taimaki Addinin Musulunci baki ɗaya”.
Daga ƙarshe bayan ya kammala jawabin kuma anyi addu'a an sallami ƴan'uwa, anfara lafiya, an kammala lafiya.
📷 MediaForumKatsina
/2025
13/09/2025